Gaisuwar Sallah Ko Shirin Zaben 2027? Shugabannin Najeriya 3 da Atiku Ya Ziyarta

Gaisuwar Sallah Ko Shirin Zaben 2027? Shugabannin Najeriya 3 da Atiku Ya Ziyarta

  • Alhaji Atiku Abubakar ya kai ziyara ga manyan shugabanni a kasar nan ciki har da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya yi ikirarin cewa ya kai ziyarar ne domin gaishe da shugabannin kasar a lokacin bukukuwan Sallah
  • Duk da ikirarin da ya yi, ziyarar ta janyo ce-ce-ku-ce kan ko ya fara neman kawaye ne a yayin da zai tsaya takara a babban zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A wani mataki da ya haifar da cece-kuce game da aniyarsa ta siyasa, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya fara ziyarar wasu fitattun shugabannin kasar.

Duk da cewa Atiku ya ce ya kai ziyarar ne domin taya su murnar Sallah, akwai rade-radin cewa mai yiwuwa tsohon mataimakin shugaban kasar ya fara yunkurin kulla kawance ne kafin zaben 2027 mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Atiku na shirya wani abu": 'Dan takaran PDP ya ziyarci Buhari a Daura

Atiku ya ziyarci IBB, Abdulsalam da Buhari
Ziyarar gaisuwar Sallah da Atiku ya kai wa tsofaffin shugabannin Najeriya ta jawo magana. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Ga jerin sunayen shugabannin Najeriya da Atiku ya kai ziyara kwanan nan:

Atiku ya ziyarci Buhari a Daura

Mun ruwaito cewa Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, jihar Katsina, a ranar Asabar, 22 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake watsi da masu alakanta ziyarar da shirin siyasa, Atiku ya ce ya je Daura ne domin taya shugaban kasa murnar bikin Sallah.

"Bisa rakiyar wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar mu ta PDP, mun je gidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na Daura domin kai ziyarar ban girma da murna bikin Sallah."

- In ji sanarwar Atiku a shafinsa na X.

Atiku ya ziyarci Janar Babangida a Minna

A ranar Laraba, 19 ga watan Yuni, muka ruwaito cewa Atiku ya gana da tsohon shugaban kasa na mulkin soja IBB a Minna, jihar Neja.

Kara karanta wannan

Sallah: Atiku ya kai ziyara ga IBB da Janar Abdulsalami a Minna, hotuna sun bayyana

An kuma bayyana wannan ziyarar ita ma a matsayin ziyarar murnar Sallah, inda hotuna ke nuna shugabannin biyu suna musayar gaisuwa.

Atiku ya gana da Janar Abdulsalami a Minna

Har ila yau, a wannan ranar Larabar, Atiku ya ziyarci tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Abdulsalami Abubakar a Minna.

Ita ma wannan ziyarar an dai kalle ta a matsayin ziyarar nuna girmamawa da kuma kai gaisuwar farin ciki a yayin bukukuwan Sallah.

Gaisuwar Sallah ko shirin zaben 2027?

Duk da an bayyana ziyarorin a matsayin gaisuwar Sallah, sai dai hakan ya jawo cece-ku-ce game da manufofin Atiku na siyasa.

Wasu mutane na ganin cewa kamar Atiku ya je kulla kawance ne da tsofannin shugabannin gabanin zaben 2027, ko kuma dai kawai ya je gaisuwar Sallah ne kamar yadda ya fada.

Matsayar Atiku kan takara a 2027

Tun da fari, mun ruwaito cewa Alhaji Atiku Abubakar ya ce mambobin PDP ne kaɗai za su yanke wanda za a ba tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027.

A cewar Atiku, idan mambobin PDP suka haɗa baki suka amince da miƙa takarar shugaban ƙasa zuwa shiyyar Kudu maso Gabas, zai mutunta matakin ya yi biyayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.