“Atiku Na Shirya Wani Abu”: 'Dan Takaran PDP Ya Ziyarci Buhari a Daura
- Rahotanni na nuni da cewa Atiku Abubakar, Aminu Tambuwal da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP sun ziyarci Muhammadu Buhari
- Kamar yadda faifan bidiyo daban-daban ya nuna, jagororin jam'iyyar adawar sun gana da tsohon shugaban kasar a gidansa na Daura
- Wannan dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan Atiku ya ziyarci Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar a jihar Neja
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Daura, Katsina - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura.
Atiku yana tare da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a yayin ganawarsu da tsohon shugaban kasar a wani faifan bidiyo da wakilin jaridar Legit Hausa ya gani.
Atiku, Tambuwal sun ziyarci Buhari
Daraktan kafofin sadarwar zamani na kungiyar Atiku The Light, Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar ya wallafa bidiyon wannan ziyarar a shafinsa na X a yau Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdul-Aziz Na'ibi ya rubuta cewa:
A yau ne mai girma Atiku Abubakar ya kai ziyarar ban girma ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a garin Daura.
"Atiku yana shirya wani babban al'amari."
Kalli bidiyon a kasa:
A wani kuma faifan bidiyon da muka gani a shafin @sir_balemoh na X, ya nuna cewa:
"Atiku ya isa gidan Muhammadu Buhari na Daura tare da Tambuwal, Dr. Mustapha Inuwa da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma"
Kalliu bidiyon a kasa:
Wannan ziyarar dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan Atiku Abubakar ya ziyarci Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar a jihar Neja, in ji rahoton The Cable.
Atiku ya ziyarci IBB da Abdulsalami
Tun da fari, mun ruwaito Atiku Abubakar ya kai ziyara ga tsofaffin shugabannin kasar Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar.
Atiku Abubakar ya kai wa waɗannan tsofaffin shugabannin ziyara ne har gidajen su da ke Minna, babban birnin jihar Neja domin taya su murnar babbar Sallah.
Jigon babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ya tabbatar da haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X a ranar Laraba, 19 ga Yunin 2024.
Asali: Legit.ng