Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku ya ziyarci Babangida a gidansa

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku ya ziyarci Babangida a gidansa

- Atiku Abubakar ya kai ziyara Jihar Neja wajen tsohon Shugaba IBB a jiya

- An sa labule tsakanin Alhaji Atiku Abubakar da Janar Ibrahim Babangida

- Kawo yanzu dai babu wanda ya san abin da manyan kasar su ka tattauna

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya kai ziyara zuwa garin Minna a ranar Litinin, 12 ga watan Oktoba, 2020.

Jaridar Vanguard ta bayyana cewa Atiku Abubakar ya sa kafa a filin jirgin saman jihar Neja da kimanin karfe 1:20 na rana, tare da ‘yan tawagarsa.

Alhaji Atiku Abubakar ya yi wata ganawa da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidansa da ke babban birnin jihar Neja.

KU KARANTA: Janar Ibrahim Babangida ya na nan bai mutu ba

Wadanda su ka yi wa tsohon mataimakin shugaban kasar sun hada da iyalinsa, wata daga cikin matansa da kuma jagoran PDP, Sanata Abdul Ningi.

Abdul Ningi ya na cikin manyan ‘yan siyasar Bauchi, kuma ya jigo ne a jam’iyyar hamayya. Ningi ya dade ya na rike da kujerar majalisar dattawa kafin 2015.

Tsohon gwamnan Neja, Dr. Muazu Babangida Aliyu ne ya yi wa su Atiku iso wajen Janar din.

Har zuwa yanzu, ba a samu cikakken labarin abin da ya kai tsohon ‘dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar wajen Ibrahim Badamasi Babangida ba.

KU KARANTA: IBB da Jonathan sun yi zama a Minna

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku ya ziyarci Babangida a gidansa
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku da Babangida Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Atiku Abubakar ne ya rikewa jam’iyyar PDP tuta a zaben 2019, ana ganin cewa zai sake jarrabar sa’arsa a 2023, lokacin da wa’adin shugaba Buhari zai cika.

Ziyarar Atiku zuwa jihar Neja ta na zuwa ne kusan mako guda bayan wani kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP ya kai wa tsohon sojan ziyara a gidansa.

Gwamna Bala Mohammed da wasu ‘yan PDP da ke kokarin dinke barakar da ke jam’iyya, sun yi zama da IBB, bayan nan sun gana da Atiku Abubakar.

Mohammed ya ce sun kai ziyarar ne domin karfafa jam'iyyar PDP kafin zabe mai zuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng