"Ba a Sauke Sanusi II Ba," Gwamnatin Kano Ta Yi Ƙarin Haske Kan Hukuncin Kotu

"Ba a Sauke Sanusi II Ba," Gwamnatin Kano Ta Yi Ƙarin Haske Kan Hukuncin Kotu

  • Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature ya ce har yanzu Muhammadu Sanusi II ne halastaccen Sarkin Kano
  • Bature ya ce Mai shari'a Muhammed Liman ya tabbatar da ingancin sabuwar dokar masarauta wadda ta tube Aminu Bayero da sarakuna huɗu
  • Haka nan kakakin gwamnan ya nuna farin cikinsa da hukuncin wanda a ganinsa ɓangaren gwamnatin ne ya samu nasara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gwamnatin Kano karƙashin Abba Kabir Yusuf ta ce hukuncin babbar kotun tarayya ya ƙara tabbatar da tuɓe Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu.

Ta ce daga nan zuwa lokacin da kotun ɗaukaka ƙara za ta yi hukuncin, Aminu Bayero da sauran sarakuna huɗu za su ci gaba da zama a matsayin waɗanda aka sauke.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Gingima-gingiman lauyoyi sun soki hukuncin kotu, sun zargi ƴan siyasa

Sanusi II da Aminu Bayero.
Gwamnatin Kano ta yi ƙarin haske kan hukuncin babbar kotun tarayya Hoto: @MasarautarKano, @ImranMuhdz
Asali: Twitter

Sakataren watsa labarai na mai girma gwamnan Kano, Sanusi Bature ne ya bayyana haka a wata hira da Channels tv cikin shirin siyasa a yau ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Abba ta yi ƙarin haske

Bature, mamban jam'iyyar NNPP ya ce:

"Ya kamata mutane su fahimci cewa hukuncin jiya ya nuna muke da nasara saboda dalilai da dama. Na farko kotu ta amince da ingancin dokar masarauta ta 2024.
"Hakan na nufin ta amince da rusa masarautu biyar tare da tsige sarakuna biyar na Kano."
"Saboda haka idan muka yi la'akari da hukuncin, ta tabbata an tuɓe rawanin Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu har zuwa lokacin da za a yi hukunci a ƙarar da muka ɗaukaka."

Idan baku manta ba mai shari'a Liman na babbar kotun tarayya ya soke duk matakan da gwamna ya ɗauka bayan fara aiki da sabuwar dokar masarauta 2024.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Babban lauya ya bayyana sahihin Sarkin Kano

Amma a cewarsa, hukuncinsa bai shafi dokar ba illa iyaka ya soke duk abin da Abba Kabir ya yi wajen aiwatar da ita kamar dawo da Sanusi II.

To sai dai a fassarar Bature, tun da har alƙalin bai haramta dokar ba, to ya tabbata cewa Muhammadu Sanusi II ne sahihin Sarkin Kano.

Wani ɗan Kwankwasiyya ya shaidawa Legit Hausa cewa hukuncin da Liman ya yanke yana da ɗaure kai.

Sa'idu Abdullahi, mazaunin Hotoro a Kano ya kafa hujja da cewa babu ruwan babbar kotun tarayya da sha'anin sarauta.

"Mutane sun sani akwai wasu ƴan siyasa a nan Kano da Abuja waɗanda ke kunno wannan wutar, burinsu Kano ta hargitse kuma in sha Allahu ba za su cimma nasara ba.
"Amma maganar sarauta mun san Sanusi II ne sarkinmu tunda ita kanta kotun ba ta haramta dokar da majalisa ta zartar ba," in ji shi.

Kano: Falana ya soki hukuncin shari'ar sarauta

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Gwamna Abba na cikin Matsala, an bayyana sahihin Sarkin Kano

A wani rahoton kuma Femi Falana ya soki hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a shari'ar sarautar Kano, ya ce akwai ruɗani.

Fitaccen lauyan mai rajin kare haƙƙin ɗan adam ya ce hukuncin yana da ɗaure kai domin kotun koli ta hana kotunan tarayya tsoma baki a sha'anin sarauta

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262