Kano: Bidiyon Buldoza Ya Ja Hankalin Mutane Yayin da Abba Ke Shirin Rusa Fadar Aminu

Kano: Bidiyon Buldoza Ya Ja Hankalin Mutane Yayin da Abba Ke Shirin Rusa Fadar Aminu

  • Rikicin sarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero ya ɗauki sabon salo yayin da aka fara shirin rusa ƙaramar fada
  • Wani bidiyo da ya bazu a soshiyal midiya ya nuna yadda gwamnatin Kano ta tura motocin Buldoza zuwa fadar da Mai martaba Aminu ke ciki
  • Wannan lamari dai ya ja hankalin ƴan Najeriya, inda suka fara martani kan yunkurin Abba na rusa wani sashin ƙaramar fada da ke Nassarawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Ƴan Najeriya sun fara raddi kan wani bidiyo da ake zargin Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirye-shiryen rusa fadar da Aminu Ado Bayero ke ciki.

An ga motocin Buldoza masu rusau da motocin da ke kwashe kaya a faifan bidiyon, wanda ake zargin gwamnatin Kano ta tura su ne zuwa ƙaramar fadar Nassarawa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun aikawa Gwamna Abba amsar umarnin tuge Aminu Ado daga fadar Nassarawa

Abba da Aminu Ado Bayero.
Mutane sun mayar da martani yayin da Abba Kabir ya fara shirin rusa fadar Aminu Hoto: @Hrhbayero @Kyusufabba
Asali: Twitter

Meyasa Abba zai rusa fadar Nassarawa?

Idan ba ku manta ba Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na Kano, Haruna Dederi ya ce gwamnati ta gama shirin gyara wani sashen fadar, wanda ya haɗa har da katanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dederi ya bayyana haka ne a wurin taron manema labarai a babban birnin jihar Kano ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni.

Kalaman kwamishinan shari'a na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan babbar kotun tarayya ta soke matakin Abba Kabir na sake naɗa Sanusi II kan karagar sarauta.

Kotun ta ce sabuwar dokar masarautar Kano 2024 tana nan daram amma gwamna ya mata rashin kunya yayin tuge Aminu Ado da naɗa Muhammadu Sanusi II.

Mutane sun yi raddi bayan ganin buldoza

Wasu ƴan Najeriya musamman kanawa sun fara raddi kan bidiyon motocin buldoza da suka tunkari ƙaramar fadar da Aminu Ado ke ciki.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba Kabir ya faɗi matakin da ya ɗauka kan hukuncin soke naɗin Sanusi II

Hassan ya ce:

"Wannan lamarin ya fara komawa wasan yara, Gwamna Abba zai tafka babban kuskure."

Kamal Ɗansadau ya ce:

"Alhamdulillah mun gode Allah, hakan ya yi kyau, da alama Abba ya farka daga barci."

Ogbeni Abbey ya mayar da martani da cewa:

"Fada wuri ne na tarihi kamata ya yi a ba ta kariya, bai kamata gwamnati ta riƙa rusa wuraren tarihi da aka yi su da daɗewa saboda siyasa ba."

Abubuwa 5 daga hukuncin kotu

A wani labarin kun ji cewa Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta soke matakin dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.

Sai dai akwai muhimman bayanai a cikin hukuncin da kotun ta yanke wanda ya kamata a ce kun sani, Legit Hausa ta tattaro maku su a rahoton nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262