"Dole Ku Amayar da Abin da Kuka Ci": Gwamna Ya Juyo Kan Ciyamomi 23 da Ya Kora
- Yayin da ake ci gaba da rikicin jihar Rivers, Gwamna Siminalayi Fubara ya umarci binciken tsofaffin shugabannin kananan hukumomi
- Fubara ya ba da umarnin ne ga babban mai binciken kudi a jihar domin zama darasi ga sabbin shugabannin kananan hukumomi 23
- Wannan na zuwa ne bayan wa'adinsu ya kare a ranar 17 ga watan Yuni wanda ya haddasa rikici a fadin jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya umarci fara binciken tsofaffin shugabannin kananan hukumomi.
Fubara ya ba mai binciken kudi a jihar umarnin domin tabbatar da binciken yadda suka gudanar da mulkinsu a ƙananan hukumomi 23.
Rivers: Fubara zai binciki ciyamomi 23
Gwamnan ya bukaci sababbin shugabannin da aka naɗa da su yi aiki tukuru wurin kare martabar al'ummarsu a cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya shawarce su da kada su rika kallon kansu a kujerar a matsayin jarumai sai dai domin bautawa al'umma.
Har ila yau, gwamnan ya ce daukar matakin zai zama darasi ga sabbin shugabannin kananan hukumomin 23 da aka naɗa, Tribune ta tattaro wannan.
Rigimar da ta barke kan korar ciyamomin
Wannan na zuwa ne bayan wa'adin tsofaffin shugabannin kananan hukumomin ya kare a ranar 17 ga watan Yuni.
Sai dai hakan ya zo da tasgaro inda wasu daga cikinsu suka ce babu wanda ya isa ya kore su daga kujerunsu a ranar 17 ga watan Yuni.
Daga bisani rikici ya barke a kusan duka kananan hukumomin jihar bayan umarnin gwamnan domin su bar ofisoshinsu.
Wasu matasa da ake zargin suna tare da gwamnan sun mamaye duka sakatariyoyin kananan hukumomin inda suka fatattaki tsofaffin ciyamomin.
Rikicin ya yi sanadin mutuwar wasu mutane da dama inda daga bisani ƴan sanda suka mamaye kananan hukumomin.
Kungiya ta shawarci Fubara kan ciyamomin
A wani labarin, kun ji cewa wata kungiya a jihar Rivers ta bukaci Gwamna Siminalayi Fubara ya kafa kwamitin binciken tsofaffin kananan hukumomi a jihar.
Kungiyar ta ce akwai zarge-zarge kan yadda ciyamomin suka gudanar da mulkinsu wanda ke cike da almundahana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng