Rikici Ya Barke Bayan Gwamna Ya Kori Shugabannin Kananan Hukumomi, Sun Ja Daga

Rikici Ya Barke Bayan Gwamna Ya Kori Shugabannin Kananan Hukumomi, Sun Ja Daga

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya sallami duka shugabannin kananan hukumomi a jihar
  • Fubara ya umarci shugabannin gudanarwa da su karbi ragamar shugabancin bayan karewar wa'adinsu
  • Wannan na zuwa ne bayan wasu shugabannin kananan hukumomi sun ce ba za su bar kujerunsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara ya rusa duka shugabannin kananan hukumomi 23 a jihar Rivers.

Fubara ya dauki wannan matakin ne bayan wa'adinsu ya kare a watan Yunin 2024 da muke ciki a jihar.

Fubara ya sallami shugabannin kananan hukumomi a Rivers
Bayan Gwamna Fubara ya kori shugabannin kananan hukumomi, sun yi biris da umarninsa. Hoto: Nyesom Wike, Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Rivers: Fubara ya ba da umarni

Gwamnan ya umarci su mika dukan komai da ke hannunsu ga shugabannin gudanarwa na kananan hukumomisu, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Kwastam ta gano dabarar da dillalai suka kirkiro wajen shigo da haramtattun kwayoyi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Premium Times ta tattaro cewa gwamnan ya godewa shugabannin kan kokarin da suka yi a jihar.

"Ina son yin amfani da wannan dama wurin godewa duka shugabannin kananan hukumomi da kansiloli kan kokarinsu a Rivers."
"A madadin gwamnati da al'ummar jihar Rivers muna yi muku godiya bayan wa'adinku ya kare a jiya 17 ga watan Yuni."
"Ina umartan duka shugabannin gudanarwa na kananan hukumomi su karbi ragamar shugabancin karamar hukumar da suke wakilta."

- Siminalayi Fubara

Wannan na zuwa ne bayan rikita-rikita a aka yi ta yi kan wa'adin shugabancin kananan hukumomi a jihar.

Mafi yawan shugabannin kananan hukumomin suna tare da Ministan Abuja, Nyesom Wike tun yana mulkin jihar.

Rivers: An samu matsala bayan karewar wa'adin

Da dama daga cikinsu sun kalubalanci karewar wa'adin nasu inda suke barazana ga duk wanda ya ke shirin korarsu.

Kara karanta wannan

Bayan tsige Mamman Ahmadu, Tinubu ya ba tsohon kwamishinan Legas wani babban muƙami

Shugaban karamar hukumar Eleme, Obarilomate Ollor ya gargadi masu kokarin korarsa daga ofishinsa inda ya ce kada wani ya kuskura ya zo kusa da shi.

Har ila yau, an jibge jami'an tsaro kananan hukumomin Port Harcourt da Obio/Akpor saboda gudun barkewar rikici.

Bayan karewar wa'adin, matasa sun mamaye hedikwatar kananan hukumomin Degema da kuma Asari-Toru.

Fubara ya kalubalanci Wike a Rivers

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya soki gwamnatin Nyesom Wike kan rashin katabus a jihar.

Fubara ya ce ayyukan da ya yiwa al'ummar jihar Rivers ya fi shekaru takwas na gwamnatoci da dama da aka yi a jihar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel