Tinubu Na Shirin Sanya Dokar Ta Baci a Kano Domin Kwace Mulki? Gaskiya Ta Fito

Tinubu Na Shirin Sanya Dokar Ta Baci a Kano Domin Kwace Mulki? Gaskiya Ta Fito

  • Yayin da Rabiu Kwankwaso ke zargin Gwamnatin Tarayya kan rigimar sarautar Kano, fadar shugaban kasa ta yi martani
  • Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya karyata zargin da ake yi na shirin sanya dokar ta baci a Kano domin tuge gwamnati
  • Ya ce kwata-kwata babu wannan shiri inda ya bayyana hakan a matsayin jita-jita kawai masar tushe bare makama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan zargin Sanata Rabiu Kwankwaso game da rigimar sarautar jihar Kano.

Gwamnatin ta karyata zargin Kwankwaso kan cewa tana kokarin sanya dokar ta baci da kawar da gwamnatin Abba Kabir.

Gwamnatin Tinubu ta musanta zargin da Kwankwaso ya yi a Kano
Gwamnatin Tinubu ta yi martani kan zargin sanya dokar ta baci a Kano da Kwankwaso ya yi. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Asiwaju Bola Tinubu, Dr. Abdullahi Ganduje.
Asali: Facebook

Kano: Tinubu ya yiwa Kwankwaso martani

Kara karanta wannan

Kano: Rundunar ƴan sanda ta yi martani kan zargin Kwankwaso na sanya dokar ta ɓaci

Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatarwa The Nation cewa babu kamshin gaskiya a wannan zargi da aka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babu kamshin gaskiya kan wannan zargi na Kwankwaso, jita-jita ce kawai ake yadawa."
"Babu yadda za a yi Gwamnatin Tarayya ta sanya dokar ta baci a jiha ba tare da hannun Majalisar Tarayya ba."
"Majalisar Tarayya yanzu tana hutu babu shugaban kasar da zai tashi kawai ya sanya dokar ta baci a jiha."

- Bayo Onanuga

Zargin Kwankwaso kan sanya dokar ta baci

Wannan na zuwa ne bayan Sanata Rabiu Kwakwaso ya zargi Gwamnatin Bola Tinubu da neman dagula jihar Kano.

Kwankwaso ya zargi gwamnatin ne game da halin da ake ciki yanzu inda ya ce suna jin shawarar makiyan Kano.

Ya ce jami'an tsaron Gwamnatin Tarayya suna nuna goyon baya ga tubabben sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Kara karanta wannan

"Ana kokarin kawo mana Boko Haram," Kwankwaso ya faɗi masu shirin hargitsa Kano

Sanatan ya bayyana haka ne yayin martani kan rigmar masarautun Kano a taron kaddamar da aikin hanya a Madobi.

Kwankwaso ya yabawa Abba Kabir

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya yabawa Abba Kabir wurin kawo ayyukan ci gaba a jihar Kano.

Kwankwaso ya ce gwamnan ya yi kokari duk da tsaiko da wasu makiyan Kano ke kawo masa cikin shekara daya da ya yi.

Sanatan ya ce an yi kokarin kawar da hankalin Abba Kabir a cikin shekara daya da ya yi a mulkin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel