Sallah: Kwankwaso Ya Faɗawa Gwamna Abba Muhimmin Abu 1 da Ya Kamata Ya Yi a Kano

Sallah: Kwankwaso Ya Faɗawa Gwamna Abba Muhimmin Abu 1 da Ya Kamata Ya Yi a Kano

  • Rabiu Kwankwaso ya bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf shawara kan ɓangaren da ya kamata gwamnatinsa ta fi mayar da hankali
  • Jagoran Kwankwasiyya ya bayar da shawarin ne yayin da gwamnan da muƙarrabansa suka kai masa ziyarar barka da Sallah
  • Gwamna Abba ya yabawa Kwankwaso bisa taimakon da yake masa, inda ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bin tafarkin Kwankwasiyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya mayar da hankali wajen gina al'umma.

Kwankwaso ya ba shi wannan shawara ne yayin da Gwamna Abba da wasu muƙarrabansa suka kaiwa jagoran NNPP ziyarar Barka da Sallah.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bayyana hanyar da za a kawo ƙarshen tsadar rayuwa a Najeriya

Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir.
Kwankwaso ya shawarci Gwamna Abba ya mayar da hankali wajen gina al'umma Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ya yabawa gwamnan bisa ƙwazon da ya yi a shekararsa ta farko a kan kujerar mulkin Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin.

Kwankwaso ya yaba da salon mulkin Abba

An tattaro cewa Kwankwaso ya yaba da kokarin gwamna Yusuf wajen bunƙasa ilimi da karfafawa mata gwiwa da nufin inganta rayuwar mazauna jihar Kano.

Kwankwaso ya nuna jin dadinsa kan yadda Gwamna Abba ke tallafawa mata da goyon bayansu, wanda ya yi daidai da aƙidar Kwankwasiyya.

Ya buƙaci gwamnatin Abba ta kara zage dantse wajen tabbatar da tsaro, taimakawa masu ƙaramin ƙarfi da kuma gina ayyukan raya ƙasa.

Tsohon gwamnan ya ce ƙofarsa a buɗe take wajen bayar da shawarwari da kuma goyon bayan gwamnati idan hakan ta taso.

Kara karanta wannan

"Ka yafewa maƙiya," Matasan Arewa sun aike da saƙo ga Sarki Aminu Ado Bayero

Gwamna Abba ya jaddada mubaya'a ga Kwankwasiyya

A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya godewa Kwankwaso bisa shawarwari da nasihar da yake masa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na bin ƙa'idoji da aƙidar ɗarikar Kwankwasiyya domin ɗaga martabar jihar Kano da kawo ci gaba mai ɗorewa.

2027: Tinubu ya fara samun goyon baya

A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fara samun goyon baya daga shugabannin siyasa gabanin babban zaɓen 2027.

Jagororin jam'iyyar APC a shiyyar Kudu maso Kudu sun bukaci Tinubu ya sake neman takara karo na biyu a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262