"Ka Gyara Kalamanka, Kai Ba Jinin Sarauta Ba Ne": Basarake Ya Kunyata Ɗan Takarar Gwamna
- Ɗan takarar gwamna ya ji wani iri bayan basarake ya ba shi kunya a gaban jama'a kan ikirarin kasancewa jinin sarauta
- Oba na Benin, Mai Martaba Ewuare II ya ci gyaran ɗan takarar gwamnan jihar Edo a jami'yyar LP, Olumide Akpata kan kalamansa
- Hakan ya biyo bayan ziyarar ɗan takarar fadar basaraken inda ya ce shi jinin sarauta ne a fadar da ke masarautar Benin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Mai Martaba, Oba na Benin, Oba Ewuare II ya ci gyara ɗan takarar gwamnan jihar Edo, Olumide Akpata.
Basaraken ya ci gyaran ɗan takarar ne a jam'iyyar LP bayan ya bayyana kansa a matsayin jinin sarauta.
Edo: Basarake ya ci gyaran ɗan takara
Wannan na zuwa ne bayan Akpata da Peter Obi sun ziyarci basaraken a fadarsa a faifan bidiyo da Vanguard ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin ziyarar Akpata ya bayyana kansa a matsayin jinin sarauta cikin yarensa na asali da kuma turanci.
Daga bisani basaraken a cikin faifan bidiyon ya yi fatali da maganar inda ya ce Akpata ba shi da alaka da sarauta ko ta wace hanya.
"Kai jajirtaccen dan kasa ne mai kokari, amma maganar kana da alaka da masarautar nan akwai kuskure."
"Duk ƴaƴana babu mai neman takara ko wanda ya tsunduma harkar siyasa, ina son fayyace hakan ga al'umma da kuma kafofin yada labarai."
- Oba Ewuare II
Edo: Martanin Akpata ga basaraken
Yayin da yake martani, Akpata ya ce tabbas ba zai iya zama jinin sarauta ba amma kuma shi ɗan masarautar ne.
Miyagu sun farmaki dan takara a Edo
A wani labarin, kun ji cewa wasu bata gari sun farmaki dan takarar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar LP, Olumide Akpata.
Akpata ya zargi babban jami'in gwamnatin jihar da daukar nauyin harin da aka kai masa a Jami'ar Benin.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a 12 ga watan Afrilu a cikin Jami'ar yayin wani babban taro da aka gudanar ana daf da zaben jihar.
Asali: Legit.ng