"Kun Ci Rabonku": Gwamna Ya Tabbatar da Dokar Haramta Fansho ga Tsofaffin Gwamnoni

"Kun Ci Rabonku": Gwamna Ya Tabbatar da Dokar Haramta Fansho ga Tsofaffin Gwamnoni

  • Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue ya sanya hannu a dokar fansho ga tsofaffin gwamnoni da mataimakansu
  • Alia ya tabbatar da dokar haramta biyan fansho ga tsofaffin gwamnonin da mataimakansu har su mutu da ake ba su
  • Gwamnan ya ce ya dauki wannan matakin ne ba tare da bambancin siyasa ba sai domin inganta rayuwar al'ummar jihar baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Alia Hyacinth ya amince da dokar dakatar da fansho ga tsofaffin gwamnoni da mataimakansu.

Gwamnan ya sanya hannu a sabbin dokoki 10 da Majalisar jihar ta kirkira domin ci gaban jihar.

Gwamna ya dakile biyan fansho ga tsofaffin gwamnoni a jiharsa
Gwamna Alia Hyacinth na Benue ya rusa dokar biyan fansho ga tsofaffin gwamnoni da mataimakansu. Hoto: Alia Hyacinth.
Asali: Facebook

Gwamna ya dakile fanshon tsofaffin gwamnoni

Kara karanta wannan

Kotun koli ta tanadi hukunci a shari'ar da Tinubu yake yi da Gwamnoni 36

Kakakin Majalisar jihar, Aondona Dajoh ya ce sun dauki matakin ne domin inganta rayuwar al'ummar Benue, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dajoh ya ce wannan na daga himmatuwar Majalisar jihar ta 10 domin kawo dokoki da za su kawo sauyi a jihar.

Dokar biyan fansho da aka soke tana biyan tsofaffin gwamnonin da mataimakansu kowane wata daidai da albashin gwamna mai ci, Channels TV ta tattaro wannan.

Daga ciki kuma akwai N25m a matsayin alawus na gyara duk bayan shekaru hudu da kuma N15m ga tsofaffin mataimakan gwamnoni.

Gwamna Alia ya fadi musabbabin dabbaka dokar

Yayin saka hannu a dokar, Gwamna Alia ya shawarci yan jihar su cire maganar siyasa a cikin lamarin sabuwar dokar.

Ya ce an yi hakan ne domin inganta jihar ba tare da duba jami'iyyar APC ko PDP ko LP ko APGA da sauran jami'iyyu ba.

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Gwamnan ya bayyana himmatuwar gwamnatinsa wurin tabbatar da kare muradun ƴan jihar ba tare da tauye musu hakki ba ta kowace hanya.

Kotu ta hana gwamna binciken Ortom

A wani Labarin, kun ji cewa babbar kotun jihar Benue ta haramtawa Gwamna Alia Hyacinth tuhumar tsohon gwamna, Samuel Ortom.

Kotun ya ce akwai korafin Ortom da ke gaban kotun wanda ta sa dole a dakatar da binciken har sai bayan duba kan korafin.

Wannan na zuwa ne bayan Alia ya kafa kwamitin binciken Ortom kan zargin badakala da almundahana da arzikin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel