Jigon APC, Salihu Lukman Ya Nakasa Jamiyyar Bayan Ya Yi Murabus, Ya Jero Dalillai
- Jam'iyyar APC ta yi babban rashi bayan jigonta ya watsar da ita saboda rashin tsare-tsare masu amfani ga ƴan ƙasa
- Tsohon mataimakin shugaban APC a Arewa maso yamma, Salihu Lukman ya bayyana haka ne a yau Laraba 12 ga watan Yuni
- Lukman ya dade yana caccakar Gwamnatin Bola Tinubu da jam'iyya mai mulki ta APC kan rashin iya shugabanci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC a Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya yi murabus.
Lukman ya zargi jamiyyar da rashin iya shugabanci da kuma munanan tsare-tsare wanda ya jefa kasar a halin kunci.
Jigon APC ya yi murabus daga jam'iyyar
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a yau Laraba 12 ga watan Yuni a Abuja, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon darakta-janar na kungiyar gwamnonin bai fadi matakin da zai dauka na gaba ko jam'iyyar da zai koma ba.
Sai dai Lukman ya ce ya hada kai da wasu manyan shugabannin siyasa domin tunkarar zaben 2027, cewar TheCable.
"Duk da haka, mutum zai iya kasancewa a jam'iyyar APC idan Tinubu zai kawo gyara a tsare-tsare kamar yadda ainihin tsarinta ya ke."
"Batun gaskiya a yanzu kasancewa ta a jam'iyyar ba shi da amfani kuma babu bukatar na ci gaba da cusa kaina a cikinta."
"Za mu yi zama da jajirtattun ƴan Najeriya wandanda suka amince wurin bunkasa dimukradiyya da ci gabanta a Najeriya."
- Salihu Lukman
APC: Lukman ya bayyana shirinsa na gaba
Jigon APC da ke Kaduna ya ce yana da tabbacin nan gaba za a samar da shugabanni da za a kawo sauyi a rayuwar ƴan Najeriya.
Ya ce ba ya tsammanin shugabannin jam'iyyar za su aminta da hukuncin da ya yanke amma daga bisani za a hada kai domin inganta dimukradiyya a Najeriya tare gaba daya.
Jigon APC ya yi murabus a Edo
Kun ji cewa APC a jihar Edo ta samu koma baya bayan babban jigo a jam'iyyar ya yi murabus yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar.
Cif Francis Inegbeneki mataimakin shugaban jam'iyyar na mazaɓar Sanatan Edo ta Tsakiya, ya yi murabus daga jam'iyyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng