Duniya Kenan: Watanni Bayan Mutuwar Gwamna, an Maye Gurbinsa Na Shugaban Gwamnoni
- Watanni kadan bayan mutuwar Rotimi Akeredolu, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos ya karbi mukaminsa
- Sanwo-Olu ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin yankin Kudu maso Yammacin Najeriya a jiya Litinin
- Wannan na zuwa ne bayan mutuwar Akeredolu a watan Disambar 2023 a Jamus wanda aka binne shi a watan Fabrairun 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Sanwo-Olu ya maye gurbin marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a jiya Litinin 10 ga watan Yuni.
An zabi Sanwo-Olu shugaban kungiyar gwamnoni
Daily Trust ta tattaro cewa Sanwo-Olu ya zama shugaban gwamnonin ne bayan zabensa da takwarorinsa a yankin suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan Sanwo-Olu, sauran gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Lucky Aiyedatiwa daga Ondo da Dapo Abiodun na jihar Ogun.
Sauran sun hada da Seyi Makinde daga jihar Oyo da Ademola Adeleke na Osun da kuma Biodun Oyebanji na jihar Ekiti a cewar Punch.
Wannan ganawar da kuma zaben Sanwo-Olu na zuwa ne watanni hudu bayan binne tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu.
Yaushe tsohon Gwamna Akeredolu ya rasu
Idan ba ku manta ba Legit Hausa ta ruwato muku cewa Akeredolu ya rasu a watan Disambar 2023 a kasar Jamus.
Daga bisani an shirya bikin binne marigayin shi a watan Faburairun 2024 bayan watanni biyu kenan da mutuwarsa a kasar Jamus.
Sanar da mutuwarsa ke da wuya aka rantsar da mataimakinsa a lokacin, Lucky Aiyedatiwa domin ci gaba da rike ragamar jihar.
Gwamnan Legas ya yi babban rashi
A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Legas, Mista Gboyega Soyannwo ya riga mu gidan gaskiya.
Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu shi ya tabbatar da mutuwar na hannun damansa a ranar Laraba 15 ga watan Mayun wannan shekara.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Gbenga Omotosho ya fitar a ranar Laraba 15 ga watan Mayu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng