Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Tsige Ƴan Majalisa 27 da Suka Sauya Sheƙa Zuwa APC

Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Tsige Ƴan Majalisa 27 da Suka Sauya Sheƙa Zuwa APC

  • Babbar kotun jihar Ribas ta ce har yanzun ƴan majalisa 27 karƙashin jagorancin Martin Amaewhuke 'ya 'yan jam'iyyar PDP ne
  • Da yake yanke hukunci ranar Litinin, Mai Shari'a Okogbule Gbasam Okogbule Gbasam ya ce babu wata hujja da ke tabbatar da sun koma APC
  • A cewar kotun, rahoton da gidajen jaridu da Radiyo suka wallafa ba zai zama hujjar sauya sheƙa ba sai an nuna katin zama mamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Babbar kotun jihar Ribas mai zama a Fatakwal ta warware taƙaddamar da ake kan sauya sheƙar mambobi 27 na majalisar dokokin jihar.

Kotun ta bayyana cewa ƴan majalisa 27 karkashin jagorancin Martin Amaewhuke da ke goyon bayan Wike, suna nan a inuwar jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun nemi a mayar da wa'adi 1 ga shugaban ƙasa, sun faɗi adadin shekaru

Gwamna Fubara da Wike.
Kotu ta raɓa gardama kan mambobin.majalisar dokokin Rivers da suka koma APC Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, kotun ta yanke wannan hukunci ne a ƙarar da Wosa Amadi da wasu mutum uku suka shigar gabanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu ƙarar sun roki kotun ta tsige ƴan majalisar daga kujerunsu saboda sun sauya sheƙa daga PDP zuwa All Progressives Congress a watan Disamba, 2023.

Kotun Rivers ta raba gardama

A hukuncin da ya yanke, Alkalin kotun, Mai shari’a Okogbule Gbasam, ya ce har yanzu Martin Amaewhule da sauran ‘yan majalisa 26 'yan PDP ne.

Mai Shari'a Gbasam ya bayyana cewa masu ƙara sun gaza gamsar da kotu ta hanyar kawo hujjojin da za su tabbatar da ƴan majalisar sun sauya sheƙa zuwa APC.

Ya ce sauya sheƙar da ake ta ɓaɓatun ƴan majalisar sun yi, ba zai yiwu a kafa hujja da labaran jaridu ko sanarwar kafafen watsa labarai ba, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana daf da gudanar da zabe, 'yan bindiga sun harbe jigon dan takarar PDP

A cewar kotun, abubuwan da za a iya kafa hujjar sauya sheka da su sun haɗa da rijista, karɓar katin zama mamba da sauran sharuɗɗan da jam'iyya ta gindaya ga masu sauya sheƙa.

Mai shari’a Gbasam ya ci gaba da cewa, ya zama wajibi gwamnatin jihar Ribas ta bi dukkan dokokin da majalisar ta zartar domin har yanzu ‘ya’yan PDP ne.

Fubara ya sake tsokano Wike

A wani rahoton kuma rigimar siyasar jihar Rivers ta sake sauya salo tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon mai gidansa, Nyesom Wike.

Fubara ya soke daukar ma'aikata 10,000 da Wike ya yi a karshen mulkinsa inda yake zargi akwai rashin bin tsari a daukar aikin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel