Jigo a APC Ya Bayyana Abin da Ke Kokarin Wargaza Jam’iyyar a Najeriya

Jigo a APC Ya Bayyana Abin da Ke Kokarin Wargaza Jam’iyyar a Najeriya

  • Tsohon mataimakin jam'iyyar APC na kasa, Salihu Lukman ya bayyana yadda jam'iyyar APC ta dauki lalacewa a fadin Najeriya
  • Lukman Salihu ya ce a halin yanzu jam'iyyar APC tana tafka dukkan kurakuran da jam'iyyar PDP ta yi a shekarun baya
  • Ya kuma bayyana yadda shugaba Bola Tinubu ya gaza tabuka komai wajen ganin dawo da jam'iyyar APC kan turba mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Lukman Salihu ya nuna rashin gamsuwa kan yadda ake tafiyar da jam'iyyar a halin yanzu.

Lukman Salihu ya koka a kan cewa an riga an kaucewa dukkan dalilan da suka sa aka kafa jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Ganduje da APC sun samu matsala bayan babban jigo ya yi murabus daga jam'iyyar

Bola Tinubu
Jigon APC ya koka kan salon mulkin Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Lukman Salihu na cewa jam'iyyar APC ta dauki hanyar lalacewa saboda tana maimaita kurakuran da PDP ta yi a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abin da ya fara lalata APC" - Lukman

Lukman Salihu ya bayyana cewa a yanzu haka jam'iyyar APC ta fara nuna mulkin mallaka ga ƴaƴanta ta inda wasu ne kawai ke jan akalar jam'iyyar.

Ya ce ana tursasawa ƴaƴan jam'iyyar yan takara maimakon a bar su su zabi wanda suke so ya wakilci jam'iyyar.

Jigo: "APC na shirin zama irin PDP"

Lukman Salihu ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta dauki halin da PDP ta yi a baya ta inda wadanda suka ci zabe ba sa biyayya ga uwar jam'iyya.

Jigon jam'iyyar ya kara da cewa jam'iyyar APC ta kaucewa dalilin kafata na magance matsalolin ilimi, kiwon lafiya da samar da walwala.

Kara karanta wannan

Komai nisan jifa: Matashi ya shiga hannun jami'an tsaro bayan shekaru da damfara

Daga ina matsalar jam'iyyar APC ta fara?

Lukman Salihu ya fadi cewa matsalar ta fara ne daga lokacin mulkin Muhammadu Buhari inda yake nuna kamar shi kadai ne zai iya tabuka komai a lokutan zabe.

Ya kuma kara da cewa sun yi tsammanin Bola Tinubu zai kawo gyara amma lamura sun kara taɓarɓarewa a mulkinsa, rahoton the Sun Nigeria.

Saboda lalacewar lamura, Lukman Salihu ya ce ba su gane yadda Tinubu ke tafiyar da mulkin ba, yana aiki kamar ba Tinubun da suka sani a baya ba.

Jam'iyyar APC ta lashe zabe a Yobe

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta samu nasara yayin da aka sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 17 na jihar Yobe.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wacce ta sanar da sakamakon zaɓen ta ce jam'iyyar ta lashe dukkanin kujerun ƙananan hukumomi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel