Atiku Ya Dauki Zafi Kan Gori da Ake Masa, Ya Fadi Yadda Ta Ceto Siyasar Tinubu a Najeriya

Atiku Ya Dauki Zafi Kan Gori da Ake Masa, Ya Fadi Yadda Ta Ceto Siyasar Tinubu a Najeriya

  • Atiku Abubakar ya magantu kan gorin da ake masa kan taimakonsa da Bola Tinubu ya yi a siyasar Najeriya
  • Ɗan takarar shugaban kasar ya ce babu kamshin gaskiya a maganar da ake yadawa tsakaninsa da Tinubu
  • Ya ce shi ne ma ya kawowa Tinubu dauki a siyasa wanda idan da bai yi hakan ba da Bola bai kawo war haka a siyasa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana yadda ya taimaki Bola Tinubu a siyasa.

Atiku ya ce idan da bai taimaki Tinubu ba da siyasarsa ta zo karshe kuma da bai kai war haka ba.

Kara karanta wannan

"Abin da ya sa Bola Tinubu ya fi Atiku da Obi cancantar zama shugaban ƙasa a 2023"

Atiku ya fadi yadda ya taimaki Tinubu a siyasa
Atiku Abubakar ya bude aiki kan yadda ya taimaki siyasar Bola Tinubu. Hoto: Tinubu Media Office.
Asali: Facebook

Yadda Atiku ya taimaki siyasar

Dan takarar shugaban kasar ya bayyana haka yayin da ya ke martani kan cewa Tinubu ya taimake shi a siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce babu inda Tinubu ya kawo masa ɗauki lokacin takun-saka da Olusegun Obasanjo kamar yadda ake yadawa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Paul Ibe ya fitar a yau Lahadi 9 ga watan Yuni a shafin X.

Atiku ya fadi yadda ya taimaki Tinubu

Ibe ya ce mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi kuskure da ya ce Tinubu ya agazawa Atiku lokacin da ya ke shan matsi a PDP.

"Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi kuskure da ya ce Tinubu ya taimaki Atiku lokacin da ya ke fuskantar barazana a PDP."
"Maganar gaskiya ita ce Atiku ne ya taimaki Tinubu saboda yadda ya ke bin tsarin dimukradiyya da kuma bin doka da oda."

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya bankaɗo 'dalilin' ɓoye ɓoyen gwamanti kan tallafin fetur

"Idan da ba domin taimakon Atiku ba da siyasar Tinubu ta ruguje tun yana gwamnan Lagos."

- Paul Ibe

PDP ta barranta da Atiku kan hadaka

A wani labarin, kun ji cewa Jam'iyyar PDP mai hamayya ta yi martani kan jita-jitar haɗaka da sauran jam'iyyun adawa a Najeriya.

Jam'iyyar ta nesanta kanta da labarin inda ta ce babu wannan maganar amma kofa a bude take ga duk mai son shigowa.

Martanin PDP na zuwa ne bayan yawan ganawa da Atiku ke yi da sauran ƴan takarar jam'iyyun adawa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel