Jonathan Ya Bayyana Abu 1 da Zai Hana ’Yan Siyasa Zuwa Kotu Idan Sun Fadi Zabe

Jonathan Ya Bayyana Abu 1 da Zai Hana ’Yan Siyasa Zuwa Kotu Idan Sun Fadi Zabe

  • Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya koka kan yadda kotuna suka lalace a fadin Najeriya
  • Shugaba Jonathan ya kuma bayyana yadda hukumar zabe ta kasa za ta taimaka wajen tsaftace kotunan Najeriya
  • Jonathan ya yi bayanin ne a jiya Talata yayin kaddamar da babban kotun jihar Delta da aka gina a birnin Asaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi magana kan yadda kotuna ke taimakon 'yan siyasa idan sun fadi zabe.

Tsohon shugaba kasar ya bayyana haka ne a jihar Delta yayin bude babban kotun jihar a jiya Talata.

Shugaba Jonathan
Goodluck Jonathan ya fadi yadda za a kawo gyara a harkar shari'a. Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a yayin bikin bude kotun, an raba motoci kirar Toyota Prado SUV guda 20 ga alkalan jihar.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta hana Alkalai zaman kotu saboda yajin aiki a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Adalci zai hana 'yan siyasa zuwa kotu"

Shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana cewa adalci da alkalai za su yi a lokutan shari'a zai hana yan siyasa da dama shigar da kara.

A cewarsa, duk wanda ya san idan ya fadi zaɓe kotu ba za ta ba shi nasara ba, to lallai ba zai shigar da kara domin kwace kujerar da bai samu ba.

Goodluck Jonathan ya kuma tabbatar da cewa hakan zai rage shigar da ƙara da 'yan siyasa ke yi da kashi 50%, rahoton Vanguard.

Jonathan: "Yadda INEC za ta tsaftace kotuna"

Shugaba Jonathan ya bayyana cewa hukumar zabe ta kasa (INEC) tana da rawar da za ta taka wajen kawo gyara a harkar shari'a a Najeriya.

Tsohon shugaban kasar ya ce yawanci masu shigar da kara bayan zabe suna kafa dalili ne da cewa ba a yi sahihin zabe ba.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya fadi muguwar illar da bukatar NLC za ta yiwa ma'aikata

Saboda haka ne ma ya ce kusan kashi 50% na masu zuwa kotu suna kafa dalili da cewa an yi maguɗi a harkar gudanar da zabe.

A ƙarshe, Goodluck Jonathan ya yabawa gwamnatin jihar Delta bisa kokarin da ta yi wajen samar da kotun zamani domin inganta harkar shari'a.

Saudiyya ta hana Hajji ba da izini ba

A wani rahoton, kun ji cewa hukumomin kasar Saudiyya sun dauki mataki mai tsauri domin hana masu zuwa aikin Hajji ba tare da rijista ba.

Gwamnatin Saudiyya ta saka tarar kusan N40m ga duk wanda aka kama ya shiga filin aikin Hajji ba tare da ya mallaki katin shaida da hukuma ta tanada ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng