'Dan PDP Ya Jero Ministoci 5 da ya Kamata Tinubu Ya Yi Waje da Su a Gwamnatinsa
- Yayin da ake kiran Shugaba Bola Tinubu ya sallami wasu daga cikin Ministocinsa, jigon PDP ya jero wadanda suka fi dacewa
- Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar ya lissafo Ministoci biyar da ya kamata Tinubu ya sallama saboda rashin yin katabus
- Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban kasar ya sha alwashin sallamar duk wani Minista da ya gaza yin wani abu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar PDP, Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar ya jero Ministocin da ya kamata Bola Tinubu ya kora a gwamnatinsa.
Abdul-Aziz Na'ibi ya bayyana cewa akwai Ministoci da dama da ba su tabuka komai ba yayin da Tinubu ya cika shekara daya kan mulki.
Jigon PDP ya bukaci korar Ministocin Tinubu
Jigon PDP ya bayyana haka a yau Talata 4 ga watan Yuni a shafinsa na X inda ya jero sunayen Ministoci guda biyar da suka gaza.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Sunayen Ministocin Tinubu guda biyar da ba su tabuka komai ba a gwamnatinsa."
"1. Ministan Matasa
2. Ministan Makamashi
3. Ministan Albarkatun Ruwa
4. Ministan Tsaro
5. Ministar Harkokin Mata."
- Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar
Barazanar da Tinubu ya yiwa Ministoci
Wannan martani na jigon PDP na zuwa ne yayin da ake yawan kiran Tinubu da ya sallami wasu daga cikin Ministocinsa.
Shugaba Tinubu da kansa ya ce zai sallami duka wadanda basu tsinana komai ba a cikin shekara daya da ya yi a gwamnati.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da kungiyar Arewa Consultative Forum a birnin Abuja a makon jiya.
APC ta gudanar da addu'o'in ga Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa, Gamayyar malaman addinin Kirista da dama ne aka hada domin yin addu'o'i ga Shugaba Bola Tinubu.
Malaman sun kuma yiwa kasar Najeriya addu'ar samun nasara da yaye duka matsalolinta wanda jam'iyyar APC ta reshen Benue ta dauki nauyi.
An gudanar da addu'o'in ne a gidan Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da ke birnin Makurdi a ranar Litinin 3 ga watan Yuni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng