Manyan Malaman Addini Sun Shirya Addu'o'i ga Tinubu, APC Ta Koma Neman Taimakon Allah

Manyan Malaman Addini Sun Shirya Addu'o'i ga Tinubu, APC Ta Koma Neman Taimakon Allah

  • Jam'iyyar APC a jihar Benue ta gudanar da addu'o'i na musamman ga Shugaba Bola Tinubu domin samun nasara a mulkinsa
  • Tawagar malaman addinin Kirista da dama ne suka jagoranci addu'o'in da aka gudanar a birnin Makurdi da ke jihar Benue
  • Shugaban jam'iyyar a jihar, Austin Agada ya ce sun shirya addu'o'in ne ga Tinubu da kuma rashin tsaro da yajin aikin da ake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Gamayyar malaman addinin Kirista da dama ne aka hada domin yin addu'o'i ga Shugaba Bola Tinubu.

Malaman sun kuma yiwa kasar Najeriya addu'ar samun nasara da yaye duka matsalolinta wanda jam'iyyar APC reshen jihar ta dauki nauyi.

Kara karanta wannan

Daliban Jami'a sun barke da murna yayin da gwamna ya rage 50% na kudin makaranta

APC ta tara manyan malaman addini domin addu'o'i ga Tinubu
Jami'yyar APC a jihar Benue ta yi addu'o'i na musamman ga Bola Tinubu. Hoto: Bola Tinubu Tinubu.
Asali: Facebook

Addu'o'in da APC ta yi ga Bola Tinubu

An gudanar da addu'o'in ne a gidan Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da ke birnin Makurdi a jihar a jiya Litinin 3 ga watan Yuni, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron addu'o'in da aka gudanar a cikin coci da kuma fili ya samu halartar shugabannin jam'iyyar APC da kuma mambobinta da dama.

Shugaba Tinubu ya shekara a mulki

Shugaban jam'iyyar APC a jihar, Austin Agada ya ce an gudanar da addu'o'in ne domin taya Shugaba Tinubu murnan cika shekara daya, cewar Tribune.

Agada ya ce an kuma yi addu'o'i domin neman taimakon Ubangiji wurin yaye matsalolin da ƙasar ke fama da su.

Ya ce sun roki ubangiji karin lafiya ga Tinubu domin samun kwarin guiwa da kuma matsalar yajin aiki da ake fama da shi na kungiyar kwadago.

Kara karanta wannan

Ana cikin rigimar sarautar Kano, Ganduje ya sake roƙon ƴan Najeriya

Tinubu: Musabbabin addu'o'in da APC ta yi

"An shirya gudanar da addu'o'in ne domin Tinubu da Akume da kuma kasar Najeriya baki daya bayan cika shekara daya a kan mulki."
"An yi addu'o'in domin neman taimakon Ubangiji kan rashin tsaro da tattalin arziki da kuma wannan yajin aiki na NLC da ake yi."

- Austin Agada

Agada ya kuma ba da tabbacin ci gaba da ba Tinubu goyon baya a jihar da ma yankin Arewa ta Tsakiya baki daya.

Kotu ya hana binciken Ortom a Benue

Kun ki cewa babbar kotun jiha a Benue ta yi hukunci kan shirin binciken tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom.

Kotun ta haramtawa Gwamna Alia Hyacinth ci gaba da gudanar da bincike kan gwamnatin Ortom har sai an kammala bincike.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.