Jam'iyyar PDP Ta Fadi Lokacin da Za Ta Dawo Kan Mulkin Najeriya
- Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sha alwashin dawowa kan madafun ikon ƙasarar nan a shekarar 2027 da ke tafe
- Muƙaddashin shugaban jam'iyyar, gwamnoninta da masu ruwa da tsaki na PDP ne suka sha wannan alwashin a birnin Umuahia, babban birnin jihar Abia
- Jiga-jigan na PDP sun taru a birnin ne domin murnar cikar shekara 76 na shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar, Sanata Adolphus Wabara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Abia - Jam'iyyar adawa ta PDP da masu ruwa da tsakinta sun sha alwashin dawowa kan mulkin ƙasar nan a shekarar 2027.
Muƙaddashin shugaban jam'iyyar, Ambassada Umar Damagum da shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar, Sanata Adolphus Wabara suka bayyana hakan a birnin Umuahia, babban birnin jihar Abia.
Gwamnonin PDP da masu ruwa da tsakin sun bayyana hakan ne ranar Asabar, yayin bikin cikar shekara 76 na Adolphus Wabara, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar PDP ta mulki ƙasar nan tun daga shekarar 1999 lokacin da aka koma mulkin dimokuraɗiyya zuwa shekarar 2015 lokacin da jam'iyyar APC ta ƙwace mulki a hannunta.
Yaushe PDP za ta dawo kan mulkin Najeriya?
Da yake magana a madadin gwamnonin PDP, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa PDP za ta dawo kan mulkin ƙasar nan a shekarar 2027.
A nasa jawabin, muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP, Ambassada Umar Damagum, ya yaba da irin gudunmawar da Wabara ya ba jam'iyyar PDP.
Ya yi nuni da cewa jam'iyyar PDP na da ƙarfin gaske a yankin Kudu maso Kudu, inda ya nuna ƙwarin gwiwar cewa waɗanda suka fice daga jam'iyyar za su dawo kafin shekarar 2027.
"Dukkanin waɗanda suka fice daga jam'iyyar PDP za su dawo kafin 2027. Jam'iyyar PDP za ta ƙwace abin da yake mallakinta ne."
"PDP za ta dawo da ƙarfinta kuma za ta samu nasara."
- Umar Damagum
Abin da zai sa Peter Obi ya koma PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Peter Obi a matsayin shugaban ƙasa a 2023, Akin Osuntokun, ya yi magana kan yiwuwar ɗan takarar ya koma jam'iyyar PDP.
Akin Osuntokun ya bayyana cewa Peter Obi zai koma jam'iyyar PDP ne kawai idan za a ba shi tikitin yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng