Aiki Ja: Gwamna Ya Sallami Ma'aikata 10,000 da Mai Gidansa Ya Ɗauka, Ya Zargi Badaƙala

Aiki Ja: Gwamna Ya Sallami Ma'aikata 10,000 da Mai Gidansa Ya Ɗauka, Ya Zargi Badaƙala

  • Rigimar siyasar jihar Rivers ta sake sauya salo tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon mai gidansa, Nyesom Wike
  • Fubara ya soke daukar ma'aikata 10,000 da Wike ya yi a karshen mulkinsa inda yake zargi akwai rashin bin tsari a daukar aikin
  • Gwamnan ya sha alwashin daukar sababbin ma'aikata tare da bin duka tsarin da ya dace ba tare da nuna wariya ko fifiko ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Yayin da rikicin siyasar jihar Rivers ke kara ƙamari, Gwamna Siminalayi Fubara ya ballo aiki.

Simi Fubara ya soke daukar ma'aikata 10,000 da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ya yi a lokacin mulkinsa.

Kara karanta wannan

'Daɗi zai biyo baya' Masana sun fadi dalilin goyon bayan tsare tsaren Tinubu

Gwamnan ya dauki mataki kan ma'aikata 10,000 da Wike ya ɗauka
Gwamna Fubara ya soke daukar ma'aikata 10,000 da Wike ya yi. Hoto: Siminalayi Fubara, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Gwamna Fubara ya soke daukar ma'aikata 10, 000

Gwamnan ya ce bai amince da yadda aka bi tsarin daukar aikin ba inda ya ce akwai kura-kurai a ciki, Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya dauki dubban matasa aiki a ma'aikatun jihar domin cike gurbin wadanda suka bari da kuma inganta harkokin gwamnati.

Bayan soke daukar aikin, Fubara ya yi alkawarin daukar wasu ma'aikata cikin tsari ba tare da nuna fifiko ba a cewar Punch.

Rivers: Fubara ya zargi badaƙala game da ma'aikatan

Har ila yau, gwamnan ya nuna damuwa kan yadda aka shigar da wasu daga ƙananan hukumomi 23 saboda siyasa ba tare da bin tsari ba.

"Lokacin da muka zo mun samu badakala na daukar ma'aikata 10,000 a kananan hukumomi 23."
"An yi bincike kan wadanda aka dauka aikin inda muka gano 60% sun zarce shekarun da ake bukata."

Kara karanta wannan

Fubara v Wike: Gwamna ya bayyana yadda ya shekara yana gwagwarmaya da ubangida

"Mafi yawansu an saka sunayensu ne saboda kawai sun san wasu ƴan siyasa da suka kawo sunayensu."

- Sim Fubara

Gwamna Fubara ya taya Sanusi II murna

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya taya Mai Martaba Muhammadu Sanusi II kan komawa kujerarsa.

Fubara ya ce ya ji dadin samun labarin kokarin mayar da Muhammadu Sanusi kujerarsa a matsayin Sarki na 16.

Wannan na zuwa ne yayin aka mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerarsa a makon da ya gabata a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel