Kotu Ta Kori Ƴan APC 25, Ta Hana Su Ayyana Kansu a Matsayin Ƴan Majalisa

Kotu Ta Kori Ƴan APC 25, Ta Hana Su Ayyana Kansu a Matsayin Ƴan Majalisa

  • Yayin da rikicin siyasar jihar Ribas ke ƙara ƙamari, kotu ta hana mambobi 25 bayyana kansu a matsayin ƴan majalisar dokoki
  • Mai shari'a C. N Wali ne ya yanke hukuncin wucin gadi a ƙarar da ƴan majalisa na tsagin Gwamna Simi Fubara suka shigar gabansa
  • Wannan mataki na zuwa ne ƙasa da wata ɗaya bayan kotun ta umarci Gwamna Fubara ya daina wata mu'amalar mulki da ƴa majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Babbar kotun Ribas mai zama a Fatakwal ta hana ƴan majalisa da ke tsagin Nyesom Wike zama ko ayyana kansu a matsayin 'yan majalisar dokokin jihar.

Kotun ta bayar da umarnin wucin gadi ne a ƙarar da ƴan majalisa da ke goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara suka shigar gabanta tare da wasu mutum biyu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu na shirin gabatar da ƙarin kasafin kuɗin 2024 a majalisar tarayya

Amaewhule da Gwamna Fubara.
Kotu ta dakatar da ƴan APC daga ayyana kansu a matsayin mambobin majalisar dokokin jihar Rivers Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: UGC

Ana shari'a kan rikicin majalisar Rivers

Karar ta jero ‘yan majalisa 25 a matsayin wadanda ake kara na 1 zuwa 25 sai kuma gwamnan Ribas, Antoni Janar da babban alkalin jihar a wadanda ake kara na 26 zuwa 28.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton The Nation ya kawo cewa a kwanakin baya ranar 10 ga watan Mayu, kotun ta bayar da umarni mai kama da wannan kan ƴan majalisar karkashin Martins Amaewhule.

Kotun ta umarci gwamna, Antoni Janar da babban alkali su yanke duk wata alaƙa ta shugabanci tsakaninsu da waɗan nan ƴan majalisa.

Meyasa kotu ta kori ƴan majalisar?

Bayan ya bayar da umarnin wucin gadi jiya Laraba, mai shari'a C. N Wali ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 1 ga watan Yuli, 2024.

Alkalin ya ce ƴan majalisar za su ci gaba da zama ƙarƙashin wannan umarni har zuwa lokacin da za a karƙare shari'ar, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Mun gaji da rikici": Matasa sun ɗauki zafi, sun shiga fada sun taso sarki waje

Ƴan majalisar karkashin Martins Amaewhule sun shiga matasala ne tun lokacin da suka sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

A bayan-bayan nan Gwamna Fubara ya ayyana su a matsayin waɗanda suka rasa kujerunsu sakamakon sauya shekar da suka yi a baya.

Kotu ta soke tsawaita wa'adin ciyamomi

A wani rahoton kuma Kotun jihar Ribas mai zama a Fatakwal ta yanke hukunci kan sahihancin tsawaita wa'adin shugabannin kananan hukumomi 23.

Hakan ya biyo bayan dokar da ƴan majalisa 27 na tsagin tsohon gwamna Wike suka amince da da ita na ƙarawa ciyamomi watanni shida.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel