Tinubu Ya Fadi Wadanda Suka Gyara Masa Hanyar Zama Shugaban Kasa a 2023

Tinubu Ya Fadi Wadanda Suka Gyara Masa Hanyar Zama Shugaban Kasa a 2023

  • A yau Laraba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara da ɗarewa mulkin Najeriya bayan shugaba Muhammadu Buhari
  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana wadanda suka masa sharar fage har ya samu damar zama zaɓaɓɓen shugaban kasa a Najeriya
  • Bola Tinubu ya bayyana haka ne a yau Laraba yayin da yake kaddamar da sabon taken Najeriya a majalisar dattawan kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi bayani kan wadanda suka zama masa silar cika burinsa na zama shugaban kasar Najeriya.

A zaben shekarar 2023 Bola Tinubu ya samu nasarar zama shugaban kasa bayan kayar da manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar da Peter Obi.

Kara karanta wannan

Jerin alkawuran da Shugaba Bola Tinubu ya gagara cikawa cikin shakara 1

Shugaba Tinubu
Bola Tinubu ya bayyana yadda majalisa ta taimaka masa wajen zama shugaban kasa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Bola Tinubu a majalisar tarayya

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban kasar ya bayyana haka ne a zauren majalisar kasar yayin kaddamar da sabon taken Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan majalisar dattijai da wakilai sun tabbatar da kudirin dawo da taken kasar na shekarun baya kuma shugaban kasa ya sa hannu kan kudurin a yau.

Waɗanda suka gyara wa Tinubu hanya

A zauren majalisar, shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa yan majalisar jamhuriya ta uku ne suke share masa hanyar zama zaɓaɓɓen shugaban kasa a shekarar 2023.

Gogewa da ya samu a majalisar Najeriya a jamhuriya ta uku ita ta ba shi dama zama kwararre kan harkokin siyasa ta haduwa da gogaggun mutane.

Yaushe Tinubu ya yi aiki a majalisa?

Shugaba Bola Tinubu ya zama Sanata mai wakiltar Legas ta tsakiya a ƙarƙashin jam'iyar SDP a shekarar 1992.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu, ya fadi abin da ya sa aka gaza gyara Najeriya

Shugaban kasar ya rike muƙamin Sanata daga watan Disambar 1992 zuwa watan Nuwamban 1993 lokacin da Sani Abacha ya yi juyin mulki.

Tinubu ya yi kira ga 'yan majalisa

Saboda kyakkyawar alaka da Tinubu ya samu da majalisa tun a baya ya nuna cewa dole su cigaba da hada kai da aiki tare domin ciyar da Najeriya gaba.

Ya kuma yi kira na musamman kan cewa ya kamata yan majalisar su cigaba da kokari wajen gina dimokuraɗiyyar Najeriya.

An koka kan mulkin Tinubu cikin shekara

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar gamayyar jam'iyyun siyasa (CUPP) ta kushe gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu cikin shekara daya da ya yi.

Kakakin kungiyar ya ce yan Najeriya sun sa ran samun sauki amma reshe ya juya da mujiya, wahala kawai suke sha ta kowanne fanni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel