"Ganduje Ya Lalata Sarautar Kano", Jigon APC Ya Faɗi Abin da Zai Faru da Jam'iyyar a Arewa

"Ganduje Ya Lalata Sarautar Kano", Jigon APC Ya Faɗi Abin da Zai Faru da Jam'iyyar a Arewa

  • Jigon jami'yyar APC, Salihu Lukman ya ce tsoma bakin Gwamnatin Tarayya a sarautar Kano zai sake lalata ta a siyasance
  • Lukman ya ce tsare-tsaren da Bola Tinubu yake dauka suna ragewa jam'iyyar APC farin jini musamman a yankin Arewa
  • Wannan nan zuwa ne bayan zargin Gwamnatin Tarayya da shiga lamarin sarautar Kano tare da kokarin dawo da Aminu Ado Bayero

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC a Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya magantu kan rikicin sarautar Kano.

Salihu Muhammad Lukman ya soki Gwamnatin Tarayya game da shiga rikicin sarautar jihar bayan tuge sarki na 15, Aminu Ado Bayero.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta tona waɗanda suka shirya zanga zanga kan rusa masarauta

Jigon APC ya magantu kan rikicin sarautar jihar Kano
Jigon APC, Salihu Lukman ya ce zai yi wahala jami'yyar ta kai labari ganin yadda ta shiga rikicin sarautar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Asiwaju Bola Tinubu, Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Sarautar Kano: Jigon APC ya soki Tinubu

Jigon APC ya ce shigar gwamnatin Bola Tinubu wannan harka da lalata lamuran kasar zai kawo cikas ga jam'iyyar a yankin Arewa a 2027, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce babban kuskure ne a siyasa Gwamnatin Tarayya tayi amfani da jami'an tsaro domin neman kawo cikas a matakin gwamnatin jihar Kano, Daily Post ta tattaro.

Sanusi II: "An gyara barnar baya" - Lukman

"A matsayina na ɗan APC a Arewa maso Yamma abin takaici ne yadda Gwamnatin Tarayya ta shiga lamarin sarautar jihar Kano."
"Dalilin matakin tube sarakunan shi ne gyara barnar da Abdullahi Ganduje ya yi a jihar lokacin da yake mulkin Kano."
"Ya kamata Tinubu ya sani APC ta fadi a zabe ne saboda yadda Ganduje ya gudanar da mulkinsa a jihar."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta nemi alfarma wajen Tinubu kan Aminu Ado Bayero

- Salihu Lukman

Jigon APC ya soki Ganduje a Kano

Ya ce abin da Ganduje ya yi ya kara siyasantar da masarautu wanda a yanzu za su dawo wa'adi kamar yadda gwamnoni ke yi.

Lukman ya kara da cewa a yanzu farin jinin APC ya yi kasa a jihar Kano ama Arewa baki daya musamman saboda irin matakan APC ke dauka a kasar.

An yi harbe-harbe a karamar fadar Kano

Kun ji cewa mutane sun shiga fargaba bayan jiyo harbe-harbe a fadar Nasarawa da Mai martaba Aminu Ado Bayero yake zaune.

Hakan ya biyo bayan umarnin kotu na tuge Aminu Ado karfi da yaji daga fadar bayan tube shi a sarauta a karshen makon da ya wuce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel