APC v SDP: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Takarar Gwamnan Jihar Kogi

APC v SDP: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Takarar Gwamnan Jihar Kogi

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kogi ta zartar da hukunci kan ƙarar da jam'iyyar SDP da ɗan takararta Murtala Ajaka suka shigar
  • Kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Ado Birnin-Kudu ta tabbatar da Ahmed Usman Ododo na jam'iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar
  • Kotun ta yi fatali da ƙarar da SDP da Murtala Ajaka suka shigar bisa dalilin cewa sun kasa tabbatar da zargin da suke yi kan waɗanda ake ƙara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kogi ta tabbatar da Usman Ododo a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar.

Kotun mai mutane uku ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Ado Birnin-Kudu ta yanke hukuncinta ne a ranar Litinin, 27 ga watan Mayun 2024.

Kara karanta wannan

Rikicin manoma da makiyaya ya barke a Jigawa, an raunata mutum 5

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Kogi
Kotu ta yi watsi da karar Muritala Ajaka, ta tabbatar da Ahmed Usman Ododo matsayin gwamnan Kogi Hoto: @OfficialOAU, @AlhMuriAjaka
Asali: Twitter

Zaben Kogi: Menene hukuncin kotu?

Mai shari'ar ya bayyana cewa jam’iyyar SDP da ɗan takararta na gwamna Murtala Ajaka sun kasa tabbatar da zarge-zarge da suke yi kan waɗanda ake ƙara, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Ado Birnin-Kudu ya ce zaɓen an gudanar da shi ne bisa bin ƙa'idar dokar zaɓe, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

APC ta doke SDP a kotun zabe

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana Ahmed Usman Ododo, ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kogi da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Ahmed Usman Ododo ya samu ƙuri’u 446,237 inda ya doke Murtala Ajaka wanda ya zo na biyu da ƙuri’u 259,052, da Dino Melaye na jam'iyyar PDP wanda ya samu ƙuri'u 46,362.

Kara karanta wannan

Rikicin masarauta: 'Yan sanda sun bankado shirin tada tarzoma a Kano, sun yi gargadi

Hukuncin zaɓen gwamnan Bayelsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Bayelsa ta tabbatar da nasarar da Gwamna Douye Diri ya samu a zaɓen gwamnan jihar.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar APC da ɗan takararta, Timipre Sylva suka shigar suna ƙalubalantar nasarar da Gwamna Diri ya samu a zaɓen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng