Bola Tinubu Ya Tsige Shugaban OORBDA, Ya Naɗa Mutum 2 a Manyan Muƙamai
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauya shugabancin wasu hukumomin gwamnatin tarayya guda biyu ranar Laraba
- Tinubu ya amince da naɗin Injiniya Chukwuemeka Woke da Dokta Adedeji Ashiru a matsayin waɗanda za su jagoranci hukumomin kasar
- Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya tabbatar da wannan naɗe-naɗen a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Injiniya Chukwuemeka Woke a matsayin Darakta-Janar/shugaban hukumar kula da kwararar mai (NOSDRA).
Mista Woke, shi ne shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Ribas a lokacin mulkin tsohon gwamna, Nyesom Wike, ministan Abuja na yanzu.
Tinubu ya naɗa shugabannin NOSDRA da OORBDA
Kakakin shugaban ƙasa, Ajure Ngelale ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 22 ga watan Mayu, 2024
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar, mai girma shugaban ƙasa ya kuma naɗa Dokta Adedeji Ashiru a matsayin shugaban hukumar raya tafkin Ogun-Osun (OORBDA).
Dada Olusegun, mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin soshiyal midiya ya wallafa sanarwar naɗe-naɗen a shafinsa na manhajar X.
"Shugaban ƙasa na fatan sababbin shugabannin za su baje basira da gogewarsu wajen ɗaga martabar waɗannan hukumomi tare da riko da gaskiya a ayyukan su"
-Ajuri Ngelale.
Shugaba Tinubu ya tsige yaron Wike
Tun da farko, Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa shugaba Tinubu ya sauke yaron ministan Abuja, Chukwuemeka Woke, daga kujerar shugaban hukumar OORBDA.
Ya ɗauki wannan matakin ne bayan sukar da ya sha kan naɗin daga manyan ƙusoshin APC da ƴan Najeriya.
Mutane da dama sun fito zanga-zanga kan naɗin Woke a matsayin MD na hukumar, inda suka ce ba ɗan yankin Kudu maso Yamna ba ne.
Kakakin shugaban ƙasa ya ce Tinubu ya maye gurbin Wike da Dakta Adedeji Ashiru.
Bola Tinubu ya naɗa shugaban FRSC
A wani rahoton kuma hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) ta samu sabon shugaba bayan kammala wa'adin tsohon shugabanta Dauda Ali Biu.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin ACM Shehu Mohammed a matsayin sabon wanda zai jagoranci hukumar har na tsawon shekara huɗu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng