'Dan Majalisa Ya Faɗi Yadda Suka Shirya Tsige Sarakuna 5 da Ganduje Ya Naɗa a Kano

'Dan Majalisa Ya Faɗi Yadda Suka Shirya Tsige Sarakuna 5 da Ganduje Ya Naɗa a Kano

  • Ɗan majalisar dokokin Kano ya bayyana cewa tun ba yanzu ba suka so tsige sarakunan masarautu biyar da Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro
  • Ya faɗi haka ne yayin da ƴan majalisar suka fara zaman garambawul ga dokar masarautun da aka yi amfani da ita wajen tsige Muhammadu Sanusi II
  • A cewarsa, babu wanda ya isa ya hana majalisar rushe waɗannan masarautu duk da ƴan majalisar APC ba su goyon bayan haka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Wasu daga cikin ƴan majalisar dokokin jihar Kano sun so rushe masarautun Kano kwanaki 20 bayan rantsar da Abba Kabir Yusuf.

Ɗaya daga cikin jagororin majalisar ne ya bayyana haka yayin da majalisa ta fara zaman gyara dokar da ta kirkiro masarautu biyar a jihar Kano.Majal

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da ƴan sanda sun mamaye zauren majalisa yayin da rigama ta kaure

Majalisar Kano da Gwamna Abba.
Yan majalisar dokokin Kano sun so a tsige Sarakunan Kano tun hawan Abba Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Majalisa da sababbin sarakunan Kano

Ɗan majalisar, wanda ya zanta da jaridar Daily Trust cikin kwarin guiwa, ya ce ba abin da zai hana su yi wa dokar garambawul.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa mai wakiltar Dala kuma shugaban masu tinjaye ne ya gabatar da kudirin gyara dokar (gyara a karo na 2).

Legit.ng Hausa ta kawo maku rahoton cewa kudirin ya shiga karatu na farko a zaman majalisar na yau Laraba, 22 ga watan Mayu.

Yadda Ganduje ya naɗa Sarakuna 5

Tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje ya rattaɓa hannu kan dokar wadda ta samar da masarautu biyar a ranar 5 ga watan Disamba, 2019.

Ganduje ya sake sa hannu kan dokar masarautun sa'ilin da aka mata kwakwarima a ranar 14 ga watan Oktoba, 2024, kana ya ƙara rattaba hannu a wani gyaran ranar 11 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ɗauki mataki da majalisa ta fara gyara dokar masarautun Kano

Majalisar Kano ta fara zaman gyara

Da yake ƙarin haske kan ƙoƙarin kara gyara dokar a yanzu, 'dan majalisar ya ce:

"Mun jima da shiryawa wannan gyaran kuma ina ganin Allah ne kaɗai zai iya dakatar da mu a halin yanzu.
"Mun so tsige waɗannan sarakunan kwanaki 20 kacal bayan rantsar da gwamnatin Abba to amma dai ga shi sai yanzu Allah ya yi.
"Saboda haka idan Allah ya kaimu gobe (Alhamis) zamu yi zama na musamnan domin duba gyaran da kuma amincewa da shi."

Shugaban masu rinjaye na majalisar ya shaidawa BBC Hausa cewa ƴan majalisa 12 na APC ba su goyon bayan rushe masarautun da tsige Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

An tsaurara tsaro a majalisar Kano

A wani rahoton kuma an tsaurara matakan tsaro yayin da majalisar dokokin Kano ta fara zaman gyara dokar masarautu yau Laraba, 22 ga watan Mayu, 2024.

Shugaban masu rinjaye na majalisar kuma mamba mai wakiltar Dala, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ne ya gabatar da kudirin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262