"Zamu Karɓe Wasu Jihohi," Ganduje Ya Bayyana Abubuwa 2 da APC Ta Shirya a 2027
- Dakta Abdullahi Ganduje ya ce APC ta shirya yadda za ta samu ƙarin gwamnoni da kuma nasarar Bola Ahmed Tinubu a 2027
- Shugaban APC na ƙasa ya bayyana haka a wurin taron da aka shirya domin duba nasarorin da shugaban ƙasa ya samu a shekara ɗaya
- Ganduje ya kuma umarci shugabannin APC na jihohi su yi aiki tare da gwamnoni da masu ruwa da tsaki domin buɗe ofis a kowace gunduma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam'iyya mai mulki ta shirya tsaf domin karɓe wasu jihohi a babban zaɓen 2027 mai zuwa.
Abdullahi Ganduje ya kuma ƙara da cewa jam'iyya mai mulki za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tazarcen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shirin jam'iyyar APC a Najeriya
Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana haka ne a Abuja a wurin taron da aka shirya kan nasarorin Tinubu yayin da ake shirin fara bikin cikarsa shekara ɗaya a mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Ganduje ya ce jam'iyyar na aiki ba dare ba rana domin ci gaba da samun nasara da kuma jan ragamar Najeriya zuwa tudun mun tsira.
APC ta shirya tunkarar 2027
Da yake jawabi kan zaɓen 2027 mai zuwa, shugaban APC na ƙasa ya ce:
"Duk da yanzu ba lokacin zaɓe ba ne, amma muna ci gaba da shiri a APC domin ganin mun samu ƙarin gwamnoni a 2027, sannan kuma za mi tabbatat shugaban ƙasa ya zarce zango na biyu.
"Mun kafa kwamitin sulhu da zai rarrashi ƴan uwanmu da suka fusata, za mu kafa irin wannan kwamitin a matakin jihohi, kananan hukumomi da gundumomi.
Ganduje ya ƙara da cewa tuni aka fara shirye-shiryen sauya fasalin APC ta yadda za ta zama kusa da al'umma tun daga tushe, The Sun ta rahoto.
A cewarsa, ya umarci rassan APC na jihohi su haɗa kai da gwamnoni da masu ruwa da tsaki su tabbatar an buɗe ofishin jam'iyya a kowace gunduma a faɗin ƙasar nan.
Kotu ta soke karin wa'adin ciyamomi
A wani labarin kun ji cewa Kotun jihar Ribas mai zama a Fatakwal ta yanke hukunci kan sahihancin tsawaita wa'adin shugabannin kananan hukumomi 23
Hakan ya biyo bayan dokar da ƴan majalisa 27 na tsagin Wike suka amince da da ita na ƙarawa ciyamomi watanni shida.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng