"Mutu Ka Raba": Atiku Abubakar Ya Bayyana Lokacin Yin Ritaya Daga Siyasa a Najeriya

"Mutu Ka Raba": Atiku Abubakar Ya Bayyana Lokacin Yin Ritaya Daga Siyasa a Najeriya

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa muddin yana raye ba zai taɓa yin ritaya daga siyasa ba
  • Atiku ya ce da shi aka yi gwagwarmayar kafa demokuraɗiyya a ƙasar nan kuma ba zai zuba ido yana kallo a lalata aikin da suka yi ba
  • Ya kuma buƙaci masu magana kan ko zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa su ƙara hakuri daga nan zuwa babban zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wazirin Adamawa kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba zai yi ritaya daga siyasa ba muddin yana raye.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa duk mai tunanin wata rana zai bar siyasa ya koma gefe yana kallo ana zaluntar talakawa to bai ma san abin da yake yi ba.

Kara karanta wannan

"Akwai matsala": ASUU ta sanar da shirin shiga yajin aiki a dukkan jami'o'in Najeriya

Alhaji Atiku Abubakar.
Atiku Abubakar ya ce ba zai taɓa yin ritaya daga siyasa ba har ya bar duniya Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023 ya faɗi haka ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa kwanan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe Atiku Abubakar zai ajiye siyasa?

Babban jigon PDP ya ce duk wanda ke mafarkin cewa zai jingine siyasa a yanzu to ya daina domin shi da siyasa mutu ka raba ne.

A rahoton da Leadership ta tattaro, Atiku ya ce:

"Idan wani yana tunanin za mu koma gefe guda mu ci gaba da kallon yadda ’yan Najeriya ke shan wahala kuma ana zaluntar su, to ina ganin wannan mutumin mafarki yake.
"Ban taɓa ji a raina na gaji da siyasa ba kuma ba zan taɓa gajiya ba, ku jira 2027 ku gani zan tsaya takara ko ba zan tsaya ba.
"Mu muka yi gwagwarmaya don kafa wannan tsarin dimokuradiyya kuma za mu ci gaba da tabbatar da dorewar ta. Don haka ba za mu zuba ido muna kallo komai ya lalace ba."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya nuna damuwa da harin masallaci a Kano, ya aike da saƙo ga Gwamna Abba

Yadda Atiku ya fara siyasa a Najeriya

Atiku dai ya shahara a siyasar Najeriya, tun 1989 kuma yana daya daga cikin makusantan marigayi Janar Shehu Yar’adua.

Ya shiga jam'iyyun siyasa daban-daban a Najeriya tun lokacin da ya fara siyasa kuma ya tsaya takara a lokuta da dama.

An zabe shi a matsayin gwamnan jihar Adamawa a 1998 amma daga baya Olusegun Obasanjo, ya ɗauko shi ya zama mataimakin shugaban ƙasa a ɓagas.

Gwamna Fubara ya naɗa kwamishinoni

A wani rahoton kuma kun ji cewa yayin da rikicin siyasar jihar Ribas ke ƙara tsananta, Gwamna Simi Fubara ya naɗa mutum takwas a matsayin kwamishinoni.

Majalisar dokokin jihar mai goyon bayan Fubara ta ce za ta tantance sababbin kwamishinonin da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Talata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel