Ganduje: Shirin Tsige Shugaban APC Na Ƙasa da Maye Gurbinsa Ya Gamu da Cikas

Ganduje: Shirin Tsige Shugaban APC Na Ƙasa da Maye Gurbinsa Ya Gamu da Cikas

  • Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ƙara samun goyon baya a daidai lokacin da shiyyar Arewa ta Tsakiya ta fara ƙoƙarin tsige shi
  • Jigon APC a jihar Kogi, Atiku Abubakar Isah ya ce duba da gogewar Ganduje da abotarsa ga Bola Tinubu, babu dalilin canza shi a yanzu
  • Ya ce Ganduje na da goyon bayan shugaban ƙasa da gwamnoni 23 don haka sauya shi a wannan lokacin zai haifar da rabuwar kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Wani jigon APC a jihar Kogi, Atiku Abubakar Isah, ya bayyana cewa bai kamata a maye gurbin Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa ba.

Ya ce Ganduje yana da gogewar da ake buƙata wajen jan ragamar jam'iyyar APC mai mulki saboda haka babu dalilin da zai sa a canza shi a halin yanzu.

Kara karanta wannan

"Zamu karɓe wasu jihohi," Ganduje ya bayyana abubuwa 2 da APC ta shirya a 2027

Shugaban APC na ƙasa, Ganduje.
Jigon APC ya ce bai kamata a sauya Ganduje a kujerar shugaban jam'iyya ba Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Atiku, tsohon sakataren jam'iyyar ANPP da aka rushe ya faɗi haka ne yayin hira da manema labarai a ƙarshen makon nan, jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A matsayin mamban APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya, fatana jam'iyyarmu ta samu kyakkyawan jagorancin da zai ƙara ɗaga ƙimarta kuma Ganduje yana da duk abin da ake buƙata," in ji shi.

Sauya Ganduje zai haifar da matsala?

Atiku ya ƙara da cewa abotar Ganduje ga Shugaba Bola Tinubu da kuma karfinsa na tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a cikin jam’iyyar, ya nuna shi ya fi dacewa da wannan aiki.

"Kowa ya sani cewa APC na bukatar shugaba wanda ke tare da shugaban kasa domin a shigar da manufofin ci gaba na jam'iyyar a gwamnati don ci gaban Najeriya.
"Don haka goyon bayan da shugaban APC ke samu daga Tinubu da gwamnonin jam'iyya 23 kaɗai ya nuna karɓuwar da yake da ita da kuma iya jagoranci.

Kara karanta wannan

Zargin daukar nauyin ta'addanci: Kotu ta yi hukunci kan bukatar Tukur Mamu

"Ganduje ya san aiki kuma babu wata jam’iyya da ta tsira a karkashin shugaba mai kama-karya amma duk jam’iyyar da ke da shugaba mai jan kowa a jiki kamar Ganduje to tabbas za ta ci gaba."

- Atiku Abubakar Isah

Atiku bai so a taba Ganduje a APC

Jigon ya yi watsi da yunƙurin Arewa ta Tsakiya na fito da ɗan takarar masalaha da zai maye gurbin shugaban APC na ƙasa, rahoton Punch.

A cewarsa, hakan barazana ce ga zaman lafiyar APC kuma shiyyar ba ta da ƙwarewar da ake buƙata wajen jagprontar babbar jam'iyya kamar APC.

Kwankwaso, Obi da Atiku zasu haɗa kai?

Jigon jam'iyyar PDP, Dare Glintstone Akinniyi, ya bayyana muhimmacin dawowar Peter Obi da Kwankwaso zuwa babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa.

Akinniyi, kakakin ƙungiyar matasan PDP na ƙasa ya ce sauya sheƙar Obi zuwa LP ya taimakawa APC, inda ya ce ya kamata ya canza tunani kafin 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel