Tsohon Kakakin Kamfen Atiku Ya Faɗi lokacin da Peter Obi Zai Iya Hawa Mulkin Najeriya
- Jigon jam'iyyar PDP, Daniel Bwala, ya tsokani ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party a zaɓen 2023, Mista Peter Obi
- Duk da raɗe-raɗin PDP ka iya haɗa maja da LP, Bwala ya ce a zaɓen 2039 ne kaɗai za a iya cewa Obi na da damar zama shugaban ƙasa
- Bayan haka Bwala ya kuma bayyana yadda za a ci gaba da bin tsarin karɓa-karɓa bayan Bola Ahmed Tinubu ya gama shekaru takwas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Daniel Bwala, babban jigo a jam'iyyar PDP ya ce mai yiwuwa Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2039.
Bwala, tsohon mai magana da yawun kwamitin kamfen Atiku Abubakar lokacin zaɓen 2023, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na LP zai samu dama ne nan da shekaru 15.
Jigon PDP ya yi iƙirarin cewa Obi zai samu damar ɗarewa kujerar mulkin Najeriya a 2039 bayan shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya gama shekara takwas, sannan Arewa ta karɓa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan siyasar ya bayyana haka ne a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, 2024.
Peter Obi ka iya samun dama a 2039
Bwala ya ce:
"Peter Obi zai samu damar zama shugaban ƙasa a Najeriya daga shekarar 2039 lokacin da ya cika shekara 79 a duniya ko sama da haka.
"Dalili shi ne bayan Bola Tinubu ya kammala shekaru takwas, mulki zai koma Arewacin Najeriya na tsawon shekaru 8 gabanin da sake dawowa kudu.
"A lokacin wanda ke kurarin su ne matasa zai koma cewa mu ne dattawa."
- Daniel Bwala
Zancen hadakar Obi da Atiku
Wannan kalamai na Bwala na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan Obi ya ziyarci Atiku Abubakar, jiga-jigan PDP da wasu manyan ƴan siyasa a Arewacin Najeriya.
Hakan ya kara tabbatar da yiwuwar haɗa kan ƴan adawa da nufin kawar da mulkin jam'iyyar APC a zaɓen 2027 mai zuwa.
Jonathan ya sa baki a rikicin Rivers
A wani rahoton Goodluck Jonathan ya nuna matuƙar damuwa kan rikicin siyasar da ke faruwa tsakanin Nyesom Wike da magajinsa, Siminalayi Fubara a Ribas
Tsohon shugaban ƙasar ya buƙaci a kawo ƙarshen wannan rikici yayin da alaƙa ke ƙara tsami tsakanin manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng