'Babu Ruwan NLC da Zancen Hadewar Atiku da Obi', Kungiyar Kwadago Za Ta Kawo Cikas

'Babu Ruwan NLC da Zancen Hadewar Atiku da Obi', Kungiyar Kwadago Za Ta Kawo Cikas

  • Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta ce ba ta da masaniya a kan batun tattaunawa tsakanin jam'iyyar LP da wasu jam'iyyu gabanin zaben 2027
  • A kwanakin nan ne aka samu rahoton yadda mai neman kujerar shugaban kasa a jam'iyyar LP Peter Obi ke zawarcin jiga-jigan Arewa domin hadewa wuri guda
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujerar shugaban kasar a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nuna suna kokarin hada kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) Joe Ajaero ya ce ba su da masaniyar tattaunawa tsakanin jam’iyyar LP da wasu ‘yan siyasa a kasar nan.

Kara karanta wannan

'Za a hada kai': Atiku ya bude baki a karon farko bayan zama da Peter Obi

Akwai rahotanni da ke nuni da cewa jam’iyyar LP na tattaunawa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a wani yunkurin hadewa gabanin zaben 2027.

Kungiyar NLC
NLC ta ce ba ta san da tattaunawar LP da wasu jam'iyyun ba Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Punch News ta wallafa cewa wadanda Peter Obi ya gana da su sun hada da tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, tsohon wasu ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da NLC aka samar da LP

Kungiyar kwadago ta NLC ce ta jagoranci kafa jam’iyyar LP a yunkurin samar da sauyi ga rayuwar ‘yan Najeriya.

Wannan ya sa ake zaton kungiyar na da masaniya kan yadda Peter Obi ke kai kawo wajen samar da dunkulalliyar jam’iyyar adawa kafin zaben 2027, kamar yadda Naija News ta wallafa.

NLC ta san zancen hadi kan PDP-LP?

A jawabinsa, shugaban NLC na kasa ya bayyana cewa babu wanda ya sanar da su batun tattaunawa tsakanin LP da sauran jam’iyyu.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Ka yi hankali da mutanen Arewa, Ibo sun fara gargadin Peter Obi

Tuni rahotanni ke nuna cewa tattaunawa ta fara nisa, domin a makon jiya an ji dan takarar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar na cewa akwai yiwuwar ya marawa Peter Obi baya a zaben gaba.

Za a hada kai tsakanin Atiku da Peter

Mun ba ku labarin cewa a karon farko bayan ganarsa da dan takarar shugaban kasa Peter Obi, Atiku Abubakar ya ce za a hada kai.

Atiku Abubakar shi ne tsohon mataimakin shugaban kasa a lokacin Olusegun Obasanjo, kuma tsohon mai neman kujerar shugaban kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel