Zaben 2027: Atiku Ya Faɗi Matsayarsa Kan Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a PDP

Zaben 2027: Atiku Ya Faɗi Matsayarsa Kan Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a PDP

  • Alhaji Atiku Abubakar ya ce mambobin PDP ne kaɗai za su yanke wanda za a ba tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi bayanin ganawarsa da Peter Obi da kuma shirin da suka fara domin tunkarar zaɓe na gaba
  • Ya musanta jita-jitar cewa ya yi ritaya daga siyasa bayan zaɓen 2023 yana mai cewa ba zai hana matasa su shigo a dama da su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce mambobin jam'iyyar PDP ne kaɗai za su yanke makomarsa kan tsayawa takara a zaɓen 2027.

Atiku ya bayyana cewa ya yi wuri a fara zancen ko zai sake neman zama shugaban ƙasa a babban zaɓe na gaba ko kuma zai hakura ya koma gefe.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya faɗi dalilin da zai sa ya goyi bayan Peter Obi a zaben 2027

Atiku Abubakar.
Atiku Abubakar ya tabbatar da yiwuwar haɗaka tsakanin jam'iyyun adawa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Getty Images

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a zaɓen 2023 ya faɗi haka ne yayin hira da BBC ranar Jumu'a, 17 ga watan Mayu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ganawar da ya yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi a kwanan nan ka iya zama wata alama ta yiwuwar fara shirin tunkarar zaben 2027.

Obi ya gana da Atiku, Saraki da Lamido

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Atiku ya gana da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, yayin da ya kai masa ziyara har gida a makon da ya wuce a Abuja.

Bayan Atiku, Mista Obi ya kuma ziyarci tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido lokuta daban-daban.

Da yake bayani kan waɗannan tarurruka, Atiku ya ce sun tattauna ne kan yanayin mulkin demokaraɗiyya a Najeriya da kuma yiwuwar haɗa maja.

Kara karanta wannan

"Mu taimaka masu," Ganduje ya yi magana kan mummunan harin da aka kai Masallaci a Kano

Wazirin Adamawa ya kuma yi watsi da jita-jitar cewa ba za su iya tsayawa su fitar da ɗan takara ta hanyar maslaha ba.

Atiku zai sake neman takara a 2027?

A cewarsa, idan mambobin PDP suka haɗa baki suka amince da miƙa takarar shugaban ƙasa zuwa shiyyar Kudu maso Gabas, zai mutunta matakin ya yi biyayya.

"Tun a zaɓen 2023 na bayyana ƙarara cewa a shirye nake idan jam'iyyar PDP ta amince Kudu maso Gabas su fitar da ɗan takara zamu yi biyayya," in ji shi.

Atiku ya kuma tabbatar da cewa akwai yiwuwar jam'iyyun adawa za su ƙulla ƙawance su haɗa maja gabanin zaɓen 2027 amma bai yi ƙarin haske kan lokacin da za su yi hakan ba.

Ya kuma masanta ikirarin cewa ya yi ritaya daga harkokin siyasa bayan zaɓen 2023, inda ya ce ko da bai yi ritaya daga siyasa ba, ba zai hana matasa gwada damar su ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya shirya zai tsamo sama da mutane 7,000 daga ƙangin rashin aikin yi

APC ta dakatar da ɗan majalisan Zamfara

A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta tabbatar da dakatar da ɗan majalisar Kaura Namoda da Birnin Magaji, Honorabul Aminu Sani Jaji a jihar Zamfara.

Sakataren APC na jihar, Alhaji Ibrahim Umar Dangaladima, ya ce kwamitin zartarwa ya amince da rahoton kwamitin ladabtarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262