"Ko a Jikina," Ministan Tinubu Ya Maida Martani kan Abubuwan da Ke Faruwa a Rivers

"Ko a Jikina," Ministan Tinubu Ya Maida Martani kan Abubuwan da Ke Faruwa a Rivers

  • Nyesom Wike ya mayar da martani kan jita-jitar cewa hankalinsa ya koma kan rigimar siyasar da ke faruwa a mahaifarsa jihar Ribas
  • Wike, Ministan Abuja na yanzu ya ce rikicin bai ɗauke masa hankali ba domin nan da ƴan kwanaki za a fara kaddamar da ayyukan da ya kammala
  • Wannan na zuwa ne a lokacin da kwamishinonin da ke goyon bayan Wike ke ci gaba da miƙa takardar murabus daga Gwamnatin Fubara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ko kaɗan rikicin siyasar jihar Rivers bai ɗauke masa hankali ba.

Mista Nyesom Wike ya ce idan da rikicin ya ja hankalinsa da mafi yawan ayyukan da ya zuba a Abuja ba su kai matakin da za a ƙaddamar da su ba.

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamna ya kuma ɗaga yatsa ga Wike, ya bugi kirji kan jikkata abokan gaba

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Nyesom Wike ya ce hankalinsa na kan birnin tarayya Abuja a matsayinsa na minista Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa ana ta yaɗa jita-jitar cewa Wike, tsohon gwamna jihar Ribas ya jingine aikinsa na minista, ya maida hankali kan abin da ke faruwa a Ribas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nyesom Wike ya mayar da martani

Amma ministan ya musanta wannan jita-jita a ranar Jumu'a, 17 ga watan Mayu yayin da yake rangadin duba wasu ayyuka da ake shirin kaddamarwa.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne zai buɗe ayyukan da aka kammala a wani ɓangaren bikin cikarsa shekara ɗaya a kan madafun iko wanda za a fara ranar 27 ga watan Mayu.

Da yake mayar da martani, Wike ya ce:

"Babu abin da ya ɗauke mani hankali daga aikina a matsayin ministan Abuja, idan da hankali na ya tafi wani wurin ba zaku ga wadannan ayyukan ba."

Tinubu zai kaddamar da ayyuka a Abuja

Kara karanta wannan

"Abin da ya sa na ƙona mutane suna sallah a Kano," Wanda ake zargi ya faɗi gaskiya

A cewarsa, Shugaban Ƙasa zai shafe kwanaki tara yana buɗe ayyukan da aka kammala a birnin tarayya Abuja, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Wannan kalamai na Wike na zuwa ne a lokacin da kwamishinonin da ke goyon bayansa suka yi murabus daga muƙamansu a gwamnatin jihar Ribas.

Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa aƙalla kwamishinoni biyar ne suka ajiye aiki a Gwamnatin Siminalayi Fubara.

Fubara ya zargi Wike da cin bashi

A wani rahoton kuma, Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa tsohon gwamna Nyesom Wike ta tarawa jihar tulin bashi.

Ya ce yanzu haka ‘yan kwangila su na ta neman gwamnatinsa ta biya cikon kudin kwangilar ayyukan da suka aiwatar wanda ya kai biliyoyin Naira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262