Jita Jita Ta Yawaita Yayin da Peter Obi Ya Gana da Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa

Jita Jita Ta Yawaita Yayin da Peter Obi Ya Gana da Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya kai ziyara ta musamman ga tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido
  • Wannan ziyara na zuwa ne a daidai lokacin da ake jita-jitar tsohon gwamnan Anambra na shirin komawa jam'iyyar PDP
  • Lamarin dai ya ja hankalin ƴan Najeriya waɗanɗa galibi ke ganin wannan ci gaba ne da zai iya haifar da sakamako mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a inuwar jam'iyyar LP ya gana da tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigon PDP, Sule Lamido.

Mista Obi ya gana da Lamido ne yayin da ya kai masa ziyara har gida a birnin tarayya Abuja ranar Litinin, 13 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Matsala ga Tinubu yayin da Atiku Abubakar ya gana da Peter Obi, bayanai sun fito

Obi ya gana da Sule Lamido.
Tsohon gwamnan Anambra ya kai wa Sule.Lamido ziyara Hoto: @ImranMuhdz
Asali: Twitter

Sule Lamido babban jigo ne a Peoples Democratic Party (PDP) wanda bai taɓa sauya sheƙa daga jam'iyyar don ya cimma wani burinsa na siyasa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Obi ya ziyarci Sule Lamido?

Wannan ziyara da Peter Obi ya kai wa tsohon gwamnan jihar Jigawa na zuwa ne yayin da raɗe-raɗin zai koma jam'iyyar APC ke ƙara yaɗuwa a Najeriya.

An fara jita-jitar Obi na ƙoƙarin sake komawa PDP ne yayin da rigingimun cikin gida suka dabaibaye jam'iyyar Labour Party ta ƙasa.

A cewar rahoton jaridar Vanguard, ziyarar da tsohon gwamnan Anambra ya kai wa takwaransa na Jigawa ta sirri ce, bisa haka babu wani ƙarin bayani kan abin da suka tattauna.

Wani mai amfani da kafafen sada zumunta, Imran Muhammad, ya wallafa hoton Obi tare da Sule Lamido a manhajar X da aka fi sani da Twitter ranar Litinin kuma ƴan Najeriya sun faɗi ra'ayoyinsu.

Kara karanta wannan

Babban jigo kuma mamban kwamitin amintattun PDP ya sauya sheƙa zuwa APC

Martanin wasu ƴan Najeriya kan ziyarar Obi

"Peter Obi ya ziyarci tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido a gidansa na Abuja domin tattaunawar sirri," in ji shi.

Wani shafi mai suna @Northerner0 ya mayar da martani da cewa:

"Ku bar shi idan ya ga dama ya ziyarci dukkan ƴan siyasar ƙasar nan ba abin da zai samu a 2027."

Shafi'i Hamidu ya ce:

"Babu maƙiyi na har abada sai dai manufa, ina fatan zamu ɗauki darasi a nan, Obi ya san abin da yake."

Fubara ya fara taso Wike a gaba

A wani rahoton kuma Gwamna Simi Fubara ya bayyana alamun zai bincike shekara 8 na tsohon uban gidansa kuma ministan Abuja, Nyesom Wike a Ribas

Yayin rantsar da sabon Antoni Janar na jihar Rivers, Fubara ya ce zai kafa kwamitin da zai binciki yadda aka tafiyar da gwamnati kafin zuwansa.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262