Rivers: Gwamnan PDP Ya Ɗauki Zafi, Ya Sha Alwashin Bincikar Ministan Bola Tinubu
- Gwamna Simi Fubara ya bayyana alamun zai bincike shekara 8 na tsohon uban gudansa kuma ministan Abuja, Nyesom Wike a Ribas
- Yayin rantsar da sabon Antoni Janar na jihar Rivers, Fubara ya ce zai kafa kwamitin da zai binciki yadda aka tafiyar da gwamnati kafin zuwansa
- Wannan na zuwa ne yayin da rikicin siyasar da ke tsakanin gwamnan da Wike ya dawo sabo a ƴan kwanakin nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya sha alwashin kafa kwamitin bincike da zai binciki tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe kafin ya hau mulki.
Simi Fubara ya bayyana hakan ne yayin rantsar da Dagogo Israel Iboroma, SAN, a matsayin Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a a gidan gwamnati da ke Fatakwal.
Gwamna Fubara v Nyesom Wike
Legit Hausa ta fahimci cewa ministan Abuja, Nyesom Wike, shi ne tsohon gwamnan jihar Ribas da ya sauka ya miƙawa Fubara a watan Mayu, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a wurin rantsar da sabon Antoni Janar ranar Litinin, Gwamna Fubara, wanda ke takun saƙa da Wike, ya ce naɗin ya zo a lokacin da ya dace.
Ya kuma bayyana cewa jihar na cikin wani mawuyacin hali inda ta bayyana cewa ba za a iya magance rikicin siyasar da ya dabaibaye Ribas ba, Channels tv ta ruwaito.
Gwamnan ya zargi abokan hamayyarsa da yi wa gwamnatinsa zagon kasa da gangan yayin da yake fatan za a warware rigimar siyasar jihar cikin ruwan sanyi.
Gwamna Fubara zai binciki Wike
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Gwamna Fubara ya lashi takobin ɗaukar ƙwararan matakai a gaba sai dai duk abinda zai faru ya faru.
"Saboda haka dan uwana Dagogo Iboroma, kai ne sabon Antoni-Janar na jihar mu. Meyasa muka naɗa ka a wannan lokacin? Muna da abubuwa da yawa a gabanmu.
“Bari na faɗa maka, kana da shirgegen aiki a gabanka. Za mu kafa kwamitin bincike na shari'a wanda zai gudanar da bincike kan dukkan harkokin mulkin jihar mu.
"Don haka sai ka zage dantse, ba gudu ba ja da baya, ina fatan zaka kare mu. Mun san zaka kare mu saboda tarihi ya nuna baka da wata matsala, kai mutumin kirki ne mai son zaman lafiya."
- Gwamna Simi Fubara.
Tsohon minista ya koma APC
Wani rahoto ya zo mana cewa tsohon ministan makamashi da ƙarafa, Farfesa Iyorwuese Hagher, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulki a jihar Benuwai.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya karɓi tsohon ministan a hukumance ranar Litinin a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng