Rikicin Rivers: Wike Ya Ba da Haƙuri, Ya Sha Alwashin Gyara Kuskuren da Ya Tafka
- Yayin da ake ci gaba da rikicin siyasar jihar Rivers, tsohon gwamna, Nyesom Wike ya yi martani kan kuskuren da ya yi
- Wike ya ce zai yi dukkan mai yiwuwa domin gyara kuskuren da ya tafka wurin zabar Siminalayi Fubara a matsayin wanda ya gaje shi
- Ministan ya kuma nemi gafarar 'yan jihar da 'yan siyasa kan wannan babban kuskure da ya yi tare da shan akwashin gyara ta nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Tsohon gwamnan jihar Rives, Nyesom Wike ya magantu kan rikicinsa da Gwamna Siminalayi Fubara.
Wike ya ce ya yi kuskure wurin goyon bayan Fubara a matsayin gwamnan Rivers.
Wike ya ba da hakuri kan Fubara
Ya ba mutanen jihar hakuri kan kuskuren da ya tafka inda ya ce zai gyara matsalar a lokacin da ya dace, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya roki al'ummar jihar da kuma 'yan siyasar da su yafe masa kuskuren da ya yi kan goyon bayan Fubara, cewar rahoton ThisDay.
"Ina son fayyace komai a nan, ni dan Adam ne ina yin kuskure ina rokon ubangji ya yafemin, kuma ku yafemin."
"Amma zamu gyara kuskure da muka yi a lokacin da ya dace, na yi kuskure ku yafemin saboda matakin da na dauka."
- Nyesom Wike
Wike ya sha alwashin gyara kuskurensa
Ministan ya ce zai gyara kuskuren Fubara inda ya ce zai ci gaba da rikita abokan gabansa domin su ci gaba da kuskure.
Wike har ila yau, ya yi martani kan ikirarin Fubara cewa ba zai taba bautawa wani dan Adam ba a wannan mataki da yake.
Tsohon gwamnan ya yi masa martani da cewa shi daman bai taba nema ko bukatar wani ya bauta masa ba.
Secondus ya caccaki Wike kan rikicin Rivers
A wani labarin, Uche Secondus, tsohon shugaban PDP ya ce Ministan Abuja, Nyesom Wike shi ne ke kitsa rikicin siyasar da Gwamna Siminalayi Fubura ke fama da shi.
Tsohon shugaban na jam’iyyar PDP ya bayyana hakan ne a birnin Tarayya Abuja a ranar Asabar 11 ga watan Mayun 2024.
Asali: Legit.ng