"Dalilin da Ya Sa Tinubu Bai Saka Baki Kan Dambarwar Ganduje Ba", APC Ta Magantu

"Dalilin da Ya Sa Tinubu Bai Saka Baki Kan Dambarwar Ganduje Ba", APC Ta Magantu

  • Jam'iyyar APC ta yi martani kan rashin tsoma baki da Shugaba Bola Tinubu ya yi kan dambarwar shugaban APC, Abdullahi Ganduje
  • Jam'iyyar ta ce Tinubu ya fi kowa damuwa da jam'iyyar amma abubuwa sun yi masa yadda ba komai ba ne zai yi martani a kai
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jami'yyar a Arewa maso Yamma, Musa Mada ya fitar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da rigimar shugaban APC, Abdullahi Ganduje, jami'iyyar ta yi martani.

Jiga-jigan jam'iyyar APC sun bayyana dalilin da ya sa Bola Tinubu bai tsoma baki ba kan wannan lamari na Ganduje.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tausaya, ya dakakar da tsarin biyan harajin 0.5% da CBN ya kawo

APC ta fadi dalilin kin saka baki a matsalar Ganduje da Tinubu ya yi
Jami'yyar APC ta yi martani kan kin saka baki da Tinubu ya yi a dambarwar Ganduje. Hoto: Ajuri Ngelale.
Asali: Facebook

Dalilin Tinubu na yin shiru kan Ganduje

Sakataren yada labaran APC a Arewa maso Yamma, Musa Mada ya ce babu wani abin zargi kan rashin saka baki da Tinubu ya yi a lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mada ya ce tun bayan dawowar dimukradiyya a 1999, babu shugaban da ke shiga lamarin jam'iyya kamar Tinubu, cewar Punch.

"Dukkan wannan lamari na Ganduje jita-jita ce kawai, idan muka duba tun 1999 zuwa yau ba a taba samun shugaban mai son jami'iyyar kamar Tinubu ba."
"Rashin maganarsa ba shi ne bai damu da jam'iyyar ba, ya lura cewa wannan sha'anin jam'iyya ne."
"Duk lokacin da kaga an yi shiru a jam'iyya to ba ta da tasiri ne, amma idan rikici ya kunno kai to kowa na neman biyan buƙatar kansa ne da neman suna."

- Musa Mada

APC ta kare Tinubu kan matsalar Ganduje

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Mada ya ce Tinubu shi ne shugaban kasa kuma ɗan jami'yyar APC amma ba komai ba ne zai yi martani a kai saboda abubuwa sun yi masa yawa.

Wannan na zuwa ne bayan dakatar da Ganduje da wani tsagin jami'yyar ya yi a gundumar Ganduje da ke jihar Kano.

An kori shugaban APC a Zamfara

Kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC a gundumar Galadima da ke birnin Gusau sun dakatar da shugaban jam'iyyar a jihar.

Tukur Danfulani ya rasa mukaminsa ne bayan shugabannin jam'iyyar 16 daga cikin 27 sun saka hannun amincewa da korar shugaban.

Shugabannin jam'iyyar suna zargin Danfulani da rashin iya shugabanci da kuma nuna wariya a tsakanin mambobinta a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.