"Sun Lalata Komai": Tsohon Shugaban Kasa Ya Koka Yadda Aka Ruguza Ayyukansa
- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Dakta Goodluck Jonathan ya koka kan yadda aka lalata tsare-tsaren da ya kawo
- Jonathan ya ce a lokacin mulkinsa ya yi kokarin kawo ayyukan ci gaba amma bayan tafiyarsa sai da aka lalata komai
- Legit Hausa ta tattauna da wani jigon jam'iyyar PDP a Gombe kan wannan martani na Goodluck Jonathan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana yadda ya kawo abubuwan ci gaba a Najeriya.
Jonathan ya ce ya kawo tsare-tsare da zasu inganta kasar amma bayan barin mulki an lalata komai.
Ayyukan alheri da Jonathan ya kawo Najeriya
Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a bikin cika shekaru 25 na Jami'ar Igbinedion da ke jihar Edo a yau Juma'a 10 ga watan Mayu, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Goodluck ya ce ya tabbatar da ba mata guraben karatu a makarantar NDA da ke Kaduna amma ya fuskanci kalubale kan kudirin nasa.
Sai dai ya ce a matsayinsa na shugaban kasa sai da ya nemo hanyar tabbatar da ganin ya aiwatar da abin da ya yi niyya, Punch ta tattaro.
Jonathan ya bukaci a ba mata dama
Jonathan ya bukaci a ba mata dama domin tabbatar da ci gabansu a dukkan bangarorin kasar ba tare da nuna wariya ba.
"Na tuno kalubalen da mata ke fuskanta a aikin soja, a matsayina na shugaban kasa na umarci ba mata guraben karatu a makarantar NDA."
"Duk wasu ayyuka da dama da na kawo na ci gaba musamman a bangaren fasaha an lalata su."
- Goodluck Jonathan
Legit Hausa ta tattauna da jigon PDP
Legit Hausa ta tattauna da wani jigon jam'iyyar PDP a Gombe kan wannan martani na Goodluck Jonathan.
Aliyu Abdulkadir ya ce abin da ya fadi gaskiya ne ganin yadda PDP suka yi mulkin adalci.
Aliyu ya ce ko a mukin marigayi tsohon shugaban kasa Yar'adua kowa ya san yadda aka yi mulki duk da karantan lokaci da ya samu.
"Babu tantama mulkin shugabannin PDP daban ya ke da irin salon mukin jam'iyyar APC tun daga 1999 zuwa yanzu."
- Aliyu Abdulkadir
Gowon ya yabawa marigayi Yar'adua
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya yabawa tsohon shugaban kasa, marigayi Umaru Musa Yar'adua.
Gowon ya ce marigayin ya kasance mutum mai gaskiya da rikon amana wanda ba a taba samunsa da cin hanci da rashawa ba.
Wannan na zuwa ne yayin da ake bikin tunawa da marigayin bayan ya cika shekaru 14 da rasuwa a watan Mayun 2010.
Asali: Legit.ng