Ganduje da APC Sun Yi Rashi, Mambobin Jam'iyyar Sun Koma NNPP

Ganduje da APC Sun Yi Rashi, Mambobin Jam'iyyar Sun Koma NNPP

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu naƙasu a jihar Jigawa bayan dubunnan mambobinta sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar adawa
  • Mambobin na APC dai sun sauya sheƙa ne zuwa ne jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) mai adawa a jihar
  • Sun bayyana cewa sun bar tafiyar APC saboda kyakkyawan fata da ƙwarin gwiwar da suka da shi cewa NNPP za ta yi abin kirki idan aka ba ta dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Dubunnan ƴaƴan jam'iyyar APC a jihar Jigawa sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP.

Sun nuna rashin amincewarsu da rashin iya mulki da tsare-tsare marasa kyau da gwamnati mai ci ke kawowa waɗanda suka ƙara wahalar da jama'a ke sha.

Kara karanta wannan

Sojoji sun dauki mataki bayan kwashe kwanaki a kauyen da aka kashe jami'ai

Mambobin APC sun koma NNPP
Mambobin APC sun koma NNPP a Jigawa Hoto: All Progressives Congress
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar NNPP, Malam Aminu Ibrahim Ringim, shi ne ya karɓe su a birnin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminu Ibrahim ya zargi gwamnatin jihar da ta tarayya da rashin samar da wani tsayayyen shiri wanda zai amfani jama'a duk da kwashe shekara ɗaya kan mulki.

Ɗan takarar gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta shirya magance matsalar tattalin arziƙi da rashin tsaron da ake fama da ita yanzu a ƙasar nan ba.

Meyasa suka bar APC zuwa NNPP?

Da yake magana a madadin masu sauya sheƙar, Malam Abubakar Lawan Kafi ya bayyana cewa:

"Mun ɗauki wannan matakin ne domin mu nuna damuwar da muke da ita kan halin matsin da ake fama da shi da yaudarar da gwamnatin APC ke yi ta rabon tallafi ga jama'a da yawan tsare-tsare marasa kyau da ake bijirowa da su."

Kara karanta wannan

Abia: Tsohon shugaban majalisa, tsofaffin ciyamomi da ƙusoshi sun fice daga PDP

"Muna da kyakkyawan fata da ƙwarin gwiwar cewa NNPP za ta kawo sauyi mai kyau idan aka ba ta dama."
"Dukkaninmu shaida ne kan shugabanci mai kyau da ake yi a jihar Kano a ƙarƙashin NNPP."
"Mun yi amanna cewa hakan shi ne abin da zai faru a ƙasar nan idan Rabiu Musa Kwankwaso ya zama shugaban ƙasa sannan Malam Aminu Ibrahim Ringim ya zama gwamnan jihar Jigawa."

- Malam Abubakar Lawan Kafi

Ƴan majalisa sun koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Rivers ta samu gagarumin sauyi yayin da mafi yawancin ƴan majalisar suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Ƴan majalisar dokokin masu biyayya ga Wike sun sauya sheƙa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne a ranar Litinin, 11 ga watan Disamba, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng