Kotu ta Sanya Ranar Sauraren Karar da Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya Shigar

Kotu ta Sanya Ranar Sauraren Karar da Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya Shigar

  • Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta sanya ranar fara sauraren karar da shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya shigar
  • Mai Shari'a, Abdullahi Muhammad Liman ne ya sanya ranar 28 ga watan Mayu domin fara sauraren karar da Ganduje ke kalubalantar korarsa
  • Shugaban APC, Abdullahi Ganduje, ta hannun lauyarsa, Hadiza Nasir Ahmad ta nemi kotun ta soke korar da wasu bangarorin jam'iyyar sukayi a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano -Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta sanya ranar fara sauraren karar da shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya shigar.

Kara karanta wannan

EFCC ta sanya ranar miƙa Ministan Buhari da 'yarsa a gaban kotu kan zargin N2.7bn

Mai Shari'a, Abdullahi Muhammad Liman ne ya sanya ranar 28 ga watan Mayu domin fara sauraren karar.

Abdullahi Umar Ganduje
Kotu za ta fara sauraren karar da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya shigar gabanta ranar 28 ga watan Mayu Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Shugaban APC, Ganduje ya kai kara a kotu

A rahoton da Daily Trust ta wallafa, Shugaban APC, Abdullahi Ganduje na kalubalantar korarsa da shugabannin mazabar Ganduje karkashin jagorancin Basiru Nuhu Isa suka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da fari, Haladu Gwanjo, mai bawa jam'iyyar APC shawara a kan shari'a ne ya bayyana ba korar Abdullahi Ganduje a ranar 15 ga watan Afrilu, haka kuma wani tsagin APC ya kara korar Ganduje a ranar 20 ga Afrilu.

Abdullahi Ganduje na son a soke korarsa

Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya nemi kotu ta ayyana korarsa da bangarori biyu a jam'iyyar ta yi a matsayin keta hakkinsa na dan Adam.

Ya ce korar da wasu marasa goyon bayansa suka yi ba tare da ba shi damar kare kansa ba, ba dai-dai ba ne kuma ya saba doka.

Kara karanta wannan

An nemi kotu ta dakatar da Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC

Dr. Ganduje, ta hannun lauyarsa Hadiza Nasir Ahmad, na neman kotun ta soke korarsa da aka yi, kamar yadda Channels Television ta wallafa.

Mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman ya sanya ranar 28 ga watan Mayu, 2024 domin fara sauraren shari'ar.

APC: An nemi kotu ta dakatar da Ganduje

A baya kun ji cewa wani jigo a jam'iyya mai mulki ta APC, Mohammed Sa'idu Etsu ya shigar da kara kotu yana bukata a dakatar da Abdullahi Umar Ganduje daga shugaban jam'iyyar.

Mohammed Sa'idu Etsu wanda ya taba neman kujerar shugabancin jam'iyyar na ganin an karya doka wajen nada Ganduje a matsayin shugaban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.