Gwamna Fubara Ya Dira Majalisa Yayin da Ake Batun Yunkurin Tsige Shi
- Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya ziyarci majalisar dokokin jihar a daidai lokacin da rikicin siyasa ya sake kunno kai a jihar
- Fubara ya ziyarci ɓangaren majalisar ne inda Martin Amaewhule da sauran ƴan majalisar da ke adawa da shi ke gudanar da zamansu na majalisa
- Ziyarar Gwamna Fubara zuwa harabar majalisar ta zo ne sa’o’i 24 bayan da aka samu sabon ɓangare a majalisar wanda ya zaɓi sabon kakaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ziyarci harabar majalisar dokokin jihar da ke birnin Port Harcourt a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu.
Ziyarar gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake batun ƴan majalisar sun fara shirya yunƙurin tsige shi.
Gwamna Fubara a majalisar Rivers
Tashar Channels tv ta sanya wani bidiyo wanda ya nuna lokacin da gwamnan ya isa harabar majalisar dokokin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bidiyon ya nuna Mai girma Gwamna Simi Fubara tare da muƙarrabansa sun shiga cikin harabar majalisar dokokin jihar.
Meyasa Fubara ya kai ziyara majalisa?
Gwamnan yace ya je majalisar ne a matsayinsa na gwamnan jihar. Sai dai ya yi tattaki na tsawon mintuna uku a cikin harabar majalisar kafin ya tafi.
Ziyarar gwamnan ta zo ne a daidai lokacin da wani sabon rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar.
Wasu daga cikin ƴan majalisar da ke biyayya ga Gwamna Fubara sun gana a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu inda suka zaɓi Victor Oko-Jumbo, mamba mai wakiltar mazaɓar Bonny a matsayin kakakin majalisar.
An zaɓi sabon kakaki a majalisar Rivers
An zaɓi Victor Oko-Jumbo a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin mai wakilai 32 da misalin ƙarfe 10:00 na safe yayin zaman majalisar na ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2024.
Sabon kakakin ya kasance ɗaya daga cikin ƴan majalisa huɗu da suka marawa gwamnan baya a farkon rikicin siyasar jihar Rivers.
A lokacin ne dai suka zaɓi Edison Ehie a matsayin kakakin majalisar amma daga baya ya yi murabus daga zama ɗan majalisar.
Daga baya Gwamna Fubara ya naɗa Edison Ehie a matsayin shugaban ma’aikatansa.
Batun tsige Gwamna Fubara
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙananan hukumomin Najeriya (ALGON) reshen jihar Rivers, sun goyi bayan a tsige Gwamna Siminalayi Fubara na jihar.
Ƙungiyar ta kuma zargi gwamna da riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar waɗanda ya kamata su gudanar da ayyukansu da su.
Asali: Legit.ng