"Ba Za Su Iya Ba": Sanata Ibrahim Ya Jero Ministocin da Ya Kamata Bola Tinubu Ya Kora
- Sanata Jimoh Ibrahim ya shawarci Bola Ahmed Tinubu ya tashi tsaye, ya sallami wasu daga cikin ministocinsa saboda ba zasu iya ba
- Ibrahim, mamban kwamitin kasafi na majalisar dattawa ya koka cewa Tinubu ya ɗauko wasu mutane da ake zargi da cin hanci ya ɗora a gwamnatinsa
- Ya jaddada cewa shugaban ƙasar ya zo da kyawawan dabaru amma babu mutane masu gogewar da za su iya aiwatar da manufofinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Mamban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar dattawa, Jimoh Ibrahim, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kori wasu daga cikin ministocinsa.
Sanata Ibrahim ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi kan majalisar ministoci da muƙarraban Tinubu a cikin shirin siyasa a yau na Channels tv ranar Laraba.
Sanata yana so a canza ministocin Tinubu
A kalamansa, sanatan ya tura saƙo ga Tinubu da cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ya kamata ka rushe majalisar ministocin nan, ka ɗauko mutanen da aka san suna da hazaƙa, waɗannan sun cika sanyi sosai,"
Ibrahim, sanata mai wakiltar Ondo ta kudu, ya nuna damuwa kan cewa ministocin da Shugaba Tinubu ya naɗa a yanzu ba su da gogewar aiki.
A cewarsa ba ya ga rashin gogewa, ministocin ba su cancanta ba idan aka yi la'akari da halin suka jefa tattalin arzikin ƙasar kusan shekara ɗaya da rantsar da Tinubu.
Sanata ya faɗi ministocin da za a kora
Sanatan ya bayyana cewa ya kamata Tinubu ya yi tunani, ya rabu da dukkan ministocin da ake zargi da hannu a badaƙalar satar kuɗin talakawa a Najeriya.
"Idan ka gaza yin haka, to kashin kajin da ke jikinsu zai shafe ka kuma hakan zai yi wa ƙasar mu babbar illa," Sanatan ya gargaɗi Tinubu.
Ibrahim ya ce Shugaba Tinubu yana da kyawawan dabaru da manufofi amma babu tsare-tsare, inda ya koka cewa muƙarrabnasa sun murkushe dabarun.
Yadda Bola Tinubu ya kafa gwamnati
Najeriya na fama da matsin tattalin arziki wanda ya samo asali daga tagwayen matakin sabuwar gwamnati watau tuge tallafin mai da haɗe kasuwannin musayar kuɗi.
Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sun shiga ofis a watan Mayun bara tare da alƙawarin za su farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan domin ƴan Najeriya su amfana.
A watan Augusta, Bola Tinubu ya naɗa ministoci 48, watanni uku bayan ya karɓi ragamar mulki daga tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, rahoton Vanguard.
Abubuwan da suka faru a tafiyar Tinubu
A wani rahoton kuma kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya ɗauki tsawon lokaci ba a san inda ya shiga ba bayan kammala taron tattalin arziki a Saudiyya.
Legit Hausa ta tattaro muku abubuwan da suka faru tun da shugaban ƙasa ya a ƙafa ya bar ƙasar nan a watan Afrilu zuwa lokacin da ake zargin ya ɓata.
Asali: Legit.ng