"An Yi Watsi da Su": Jigon APC Ya Magantu Kan Halin da El Rufai da Yahaya Bello Ke Ciki

"An Yi Watsi da Su": Jigon APC Ya Magantu Kan Halin da El Rufai da Yahaya Bello Ke Ciki

  • Jigon jami'yyar APC, Jesutega Onakpasa ya soki yadda lamura ke gudana a cikin jami'yyar bayan nasarar da ta samu
  • Onakpasa ya koka kan halin da tsofaffin gwamnoni kamar Nasir El-Rufai da Yahaya Bello suke ciki bayan gudunmawa da suka bayar
  • Ya bukaci nemo hanyoyin dakile ɓarakar da ake fuskanta a jami'yyar domin samun nasara a zaben gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar APC, Jesutega Onakpasa ya zargi wasu 'yan siyasa da kawo matsala a cikin jami'yyar.

Barista Onakpasa ya koka kan halin da tsofaffin gwamnoni, Nasir El-Rufai da Yahaya Bello ke ciki a yanzu.

Jigon APC ya magantu kan halin da El-Rufai da Yahaya Bello ke ciki
Jigon APC ya zargi wasu a jam'iyyar kan halin da El-Rufai da Yahaya Bello ke ciki. Hoto: Nasir El-Rufai, Asiwaju Bola Tinubu, Yahaya Bello.
Asali: Facebook

Wane zargi jigon APC ya yi?

Kara karanta wannan

Ana daf da gudanar da zabe, APC da PDP sun yi barin 'yan takarar gwamna

Lauyan ya zargi wasu a jam'iyyar da kawo matsala duk da gudunmawa da tsofaffin gwamnonin suka bayar a zaben da aka gudanar a 2023, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wasu da suka kware wurin sukar jam'iyyar APC yanzu sun samu mukamai yayin da asalin masu biyayya aka watsar da su, cewar Tribune.

"Ya ku mambobin jam'iyyar APC, na kasance daga cikin kwamitin kamfe na shugaban kasa kuma lauyan kwamitin."
"Abin takaici ne yadda jam'iyyar ta dawo wurin yin amfani da mutane kuma ta watsar da su bayan amfaninsu."
"Wadanda suka ci zarafin shugaban kasa a baya a yanzu an fi basu kulawa fiye da wadanda suka kasance masu biyayya ga jam'iyyar."

- Jesutega Onakpasa

Yunkurin sauke Ganduje daga kujerar APC

Onakpasa ya bayyana damuwa kan yadda ake neman tuge shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje daga mukaminsa bayan matsalar Yahaya Bello

Kara karanta wannan

"Zai yi wahala": Lauyan APC ya fadi hanya 1 da Ganduje zai rasa muƙaminsa a jam'iyya

"Babban abin da ke damu na yanzu shi ne halin dan uwana tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ke ciki."
"Sannan Nasir El-Rufai wanda ya ba da gudunmawa sosai a zabe, bayan wasu watanni kuma sai aka dawo kan Ganduje."

- Jesutega Onakpasa

An maka shugaban APC, Ganduje a kotu

A wani labarin, tsohon mai neman takarar kujerar APC, Mohammed Sa'idu-Etsu ya bukaci kotu ta rusa nadin shugaban jam'iyyar.

Etsu ya ce an nada Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar ba bisa ka'ida ba wanda ya kamata a ce zabe ne aka shirya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.