Ba Mu Yarda a Tsige Gwamnan Rivers Ba, Jam’iyyar PDP Ta Fusata Kan Kalaman APC
- Jam'iyyar PDP ta gargadi takwararta ta APC da furta kalaman da za su tunzura jama'a da kuma kawo rashin zaman lafiya a jihar Rivers
- Tun da fari, jam'iyyar APC ta yi kira ga majalisar dokokin jihar Rivers da ta tsige Siminalayi Fubara daga kujerar gwamnan jihar
- A cewar PDP, irin wannan kalaman na APC na cike da tunzurarwa yayin da jam'iyyar ta kuma nemi 'yan sanda su tsawatarwa APC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jam'iiyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta gargadi jam'iyyar APC kan kiran da ta yi na majalisar dokokin jihar Rivers ta tsike Gwamna Siminalayi Fubara.
PDP ta dura kan 'yan majalisun Rivers
PDP a matakin kasa, ta ce irin wadannan kalaman na jam'iyyar APC ka iya tunzura jama'a kuma na iya kawo rashin zaman lafiya, jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Debo Ologunagba, sakataren yada labarai na PDP na kasa, ya ce ko su 'yan majalisar jihar da APC ke tunkaho da su bai kamata ci gaba da zama a zauren majalisar ba.
A cewar Ologunagba, kamata ya yi a wofantar da kujerun 'yan majalisar jihar da aka zaba karkashin PDP amma suka sauya sheka zuwa APC.
"Rivers ta fi karfin APC" - PDP
Don haka ya yi kira ga Sufeta Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, da ya tsawatarwa shugaban APC na jihar Rivers, Cif Tony Okocha, domin gujewa ta tashin tashina.
Kakakin jam’iyyar PDP ya ce tuni jam’iyyar ta garzaya kotu, kuma ta rubuta koke ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan batun, jaridar Premium Times ta ruwaito.
Ologunagba ya kara da cewa kamata yayi APC ta farka daga wannan mafarkin da take yi na kwace jihar Rivers daga hannun PDP domin jihar ta fi karfinta.
Fubara ya rantsar da kwamishinoni
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya sake rantsar da wasu kwamishinoni guda tara da za su yi aiki a gwamnatinsa.
Kwamishinonin dai sun yi murabus a farko domin nuna goyon bayansu ga ministan Abuja, Nyesome Wike, amma daga bisani Fubara ya sake naɗa su bayan an yi sasanci.
Asali: Legit.ng