Kungiyar ALGON Ta Goyi Bayan Kiran a Tsige Gwamnan PDP Daga Kujerarsa
- Ƙungiyar ƙananan hukumomin Najeriya (ALGON) reshen jihar Rivers ta zargi Gwamna Siminalayi Fubara da laifin yin bake-bake kan kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar
- ALGON ta hannun shugabanta na jihar, Allwell Ihunda, ta zargi gwamnan da riƙe kuɗaden da aka warewa ƙananan hukumomi 23 na jihar
- Allwell Ihunda ya kuma goyi bayan kiran da jam'iyyar APC ta yi na majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige gwamnan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Ƙungiyar ƙananan hukumomin Najeriya (ALGON) reshen Jihar Rivers ta zargi Gwamna Siminalayi Fubara da riƙe kuɗaɗen ta da aka warewa ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Ƙungiyar ALGON ta jihar ta ce matakin ya hana su gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansu.
Shugabannin ƙananan hukumomin sun bayyana cewa matakin da gwamnan ya ɗauka tamkar ya rushe ƙananan hukumomin jihar ne, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ALGON na so a tsige Gwamna Fubara
Shugabannin sun kuma nuna goyon baya kan kiran da muƙaddashin shugaban jam'iyyar APC na jihar, Tony Okocha, ya yi na majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige Gwamna Fubara.
Shugaban ALGON na jihar kuma shugaban ƙaramar hukumar birnin Port Harcourt, Allwell Ihunda, shi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba, rahoton da jaridar Leadership ya tabbatar.
Fubara: Wane zargi ALGON ta yi?
Allwell Ihunda ya bayyana cewa da gangan Gwamna Fubara ya ƙi kiran taron kwamitin asusun haɗin gwiwa wanda sai an yi shi ne kafin a sakarwa ƙananan hukumomi kuɗi.
Ihunda ya bayyana cewa gwamnan ya riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi 23 na jihar tun daga watan Afirilun 2024.
Ya ƙara da cewa ƙaramar hukumar Emouha ba ta samu na ta kason ba tun watan Maris 2024, inda ya bayyana hakan a matsayin tauye musu haƙƙi na gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansu.
Fubara ya caccaki ƴan majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminialayi Fubara, ya bayyana cewa wanzuwar ƴan majalisar dokokin jihar ta ta'allaka ne ga amincewarsa ko akasin hakan.
Gwamnan Fubara ya ce babu mambobi a majalisar jihar, yana mai bayyana cewa yana "ɗaga musu ƙafa" saboda yarjejeniyar zaman lafiya da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar.
Asali: Legit.ng