Kano: Tsohon Kwamishina Ya Yi Ikirarin Gwamna Abba Kabir Ya Amince Zai Koma APC
- Musa Ilyasu Kwankwaso ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya amince zai sauya sheƙa zuwa APC tun kafin hukuncin kotun koli
- Tsohon kwamishinan kuma jigon APC ya ce jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso bai san da lamarin ba sai daga baya
- Ya ce a halin yanzun gwamnan da tawagarsa sun bukaci ƙarin lokaci domin su kammala shirye-shiryen dawowa jam'iyya mai mulkin kasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano- Tsohon kwamishina a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi zargin cewa gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da yarjejeniyar barin jam'iyyar NNPP.
Musa Iliyasu Kwankwaso wanda ya riƙe kujerar kwamishina sau uku a Kano, ya yi iƙirarin cewa an yi yarjejeniya da gwamnan cewa zai baro tafiyar NNPP, ya dawo APC.
Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi wannan ikirarin ne yayin da yake tsokaci kan dambarwar siyasar Kano, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma ƙara da cewa wannan yarjejeniya ce ta sanya kotun ƙolin Najeriya ta ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen gwamna a Kano.
Kwankwaso ya san da yarjejeniyar Abba-APC?
A wata hira da ƴan jarida jiya Litinin a Kano, tsohon kwamishinan kuma jigon APC ya ce jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso, ba ya cikin wannan yarjejeniya.
A cewarsa, da farko babu Kwankwaso a cikin yarjejiyar da aka cimma da Gwamna Abba Kabir to amma daga baya an jawo shi ciki.
Sai dai kuma jigon ya yi gum da bakinsa kan wanda gwamnan ya zauna suka yi wannan yarjejeniya da shi.
Maganar Musa Kwankwaso kan shigowar Abba APC
"(Gwamna da tawagarsa) sun amince za su koma jam'iyyar APC a ƙurarren lokaci kuma an yi dukkan tsare-tsaren raba muƙamai na jiha da na jam'iyya.
"Sun amince da hakan ba tare da sanin ogansu (Kwankwaso) ba wanda ya nuna ɓacin ransa amma ba shi da wani zaɓi. Daga baya ya kawo sharuɗɗansa wanda ba dole a amince ba.
"Har yanzun sun gaza cika sharuɗɗan yarjejeniyar, sun nemi a ƙara masu lokaci, kusan watanni biyar domin su gama shirye-shirye, sannan su shigo APC."
- Musa Ilyasu Kwankwaso.
Ya bayyana cewa duk wani ɗan APC mai biyayya ba ya jin haushin ƴan adawa su shigo cikin jam'iyya mai mulki.
APC ta yi babban kamu a Ebonyi
A wani rahoton kuma wasu manyan jiga-jigan babbar jam'iyyar adawa PDP a jihar Ebonyi sun tattara sun koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Sylvanus Ngele, tsohon ɗan majalisar dattawa da ɗan takarar gwamna a zaɓen 2023 na cikin waɗanda suka haƙura da PDP a ranar Litinin.
Asali: Legit.ng