"Zai Yi Wahala": Lauyan APC Ya Fadi Hanya 1 da Ganduje Zai Rasa Muƙaminsa a Jam'iyya
- Lauyan jam'iyyar APC a Najeriya, Abdulkarim Kana ya yi fashin baki kan dambarwar dakatar da Dr. Abdullahi Ganduje
- Kana ya ce babu wanda ke da karfin ikon dakatar da Ganduje a jami'yyar sai kwamitin gudanarwa na jam'iyyar a halin yanzu
- Wannan na zuwa ne bayan wani tsagin jam'iyyar gundumar Ganduje da ke jihar Kano ya sake dakatar da shi a kwanakin baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Mai ba da shawara ga jami'yyar APC a bangaren shari'a, Abdulkarim Kana ya magantu kan dakatar da Abdullahi Ganduje.
Kana ya ce kwamitin gudanarwar jam'iyyar (NWC) ne kawai zai iya daukar wannan mataki kan Abdullahi Umar Ganduje.
Tsarin APC kan dakatar da Ganduje
Lauyan ya bayyana haka ne yayin hira da Channels TV a jiya Litinin 6 ga watan Mayu kan dambarwar da ake yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce kafin dakatarwar ta tabbata dole sai an bi dukkan tsare-tsaren jam'iyyar kamar yadda doka ta fayyace.
"Dole sai an bi tsare-tsaren da suka dace kafin daukar wannan mataki."
"Yayin da ake kan bincike, babu wani bangare na jam'iyyar da ke da ikon dakatar da dan APC ana kan bincike sai kwamitin NWC.".
- Abdulkarim Kana
APC ta gano wadanda suka yi aika-aika
Kana ya kara da cewa a baya hakan ya faru amma kafin yi wa kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC gyaran fuska ne a 2023.
Har ila yau, ya ce wadanda suka dakatar da Ganduje ba 'yan jam'iyyar APC ba ne kamar yadda bincike ya tabbatar.
Ya ce bayan APC ta gudanar da bincike ta tabbatar da cewa wadanda suka dauki wannan mataki ba su daga cikin shugabannin jam'iyyar gundumar Ganduje.
APC: An sake maka Ganduje a kotu
A wani labarin, an ji cewa wani mai neman kujerar Abdullahi Ganduje a Najeriya ya maka shi a kotu kan rashin bin tsari a nada shi mukamin.
Mohammed Sa'idu-Etsu ya ce kwata-kwata bai dace a nada Ganduje shugaban jam'iyyar ba, kamata ya yi a yi zabe kamar yadda doka ta tanadar.
Asali: Legit.ng