Sanata, Tsohon Ɗan Majalisa da Manyan Ƙusoshin PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

Sanata, Tsohon Ɗan Majalisa da Manyan Ƙusoshin PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

  • Abubuwa sun kara dagulewa a jam'iyyar PDP yayin da wasu manyan ƙusoshi suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a Ebonyi
  • Sylvanus Ngele, tsohon ɗan majalisar dattawa da ɗan takarar gwamna a zaɓen 2023 na cikin waɗanda suka haƙura da PDP a taron ranar Litinin
  • Wannan sauya sheƙa na zuwa ne mako ɗaya bayan mamba mai wakiltar Abakaliki ta Arewa a majalisar dokokin jihar ya koma APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ebonyi - Wasu manyan jiga-jigan babbar jam'iyyar adawa PDP a jihar Ebonyi sun tattara sun koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar har da tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Abakaliki/Izzi da ɗan takarar gwamna a zaɓen 2023, Sylvester Ogbaga.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle: APC ta fadi manufar masu son ganin EFCC ta binciki minista

PDP ta rasa manyan jiga-jigai a Ebonyi.
Tsohon ɗan majalisar tarayya da ɗan takarar gwamna sun jagoranci kusoshin PDP zuwa APC a Ebonyi Hoto: OfficialPDP, OfficialAPCNig
Asali: Facebook

Haka zalika tsohon sanata kuma tsohon mamban kwamitin ayyuka na PDP ta ƙasa (NWC), Sylvanus Nguji Ngele, na cikin manyan ƙusoshin da suka koma APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bikin sauya shekar ya gudana ne a hedikwatar karamar hukumar Abakaliki da ke Nkaliki ranar Asabar da ta gabata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Meyasa 'yan siyasar suka koma APC?

Da suke jawabi a wurin taron, manyan jagororin masu sauya sheƙar Honorabul Ogbaga da Sanata Ngele, sun ce sun hakura da tafiyar PDP ne saboda ta gaza kafa gwamna daga yankin Izzi.

A cewarsu, sun yanke shawarar komawa inuwar APC mai alamar tsintsiya domin ta cika masu burinsu na ganin ɗan yankin Izzi a kujerar gwamna

Bugu da ƙari, sun kuma bayyana nasarorin gwamnatin Francis Nwifuru a matsayin babban abin da ya ja hankalinsu suka rungumi APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Binciken Matawalle: An yi sabuwar fallasa kan masu zanga-zanga a EFCC

Yayin da suke maraba da masu sauya sheƙar, manyan masu ruwa da tsaki ciki har da ma'ajiyin APC na ƙasa, Matthew Uguru, sun yabawa musu bisa ɗaukar wannan mataki.

Sun roki masu sauya sheƙar su koma gundumomin su kuma su tabbata sun mallaki katin zama cikakken mamban APC, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Ɗan majalisa ya shiga APC daga PDP

A makon jiya ne wasu jiga-jigan PDP a ƙaramar hukumar Abakaliki ciki har da mamban majalisar dokokin Ebonyi, Victor Nwoke, suka koma APC yayin ziyarar matar gwamna, Mary-Maudlin Nwifuru.

Edo: An dakatar da ƴan majalisa 3

A wani bangaren rahoto ya zo cewa shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya dakatar da ƴan majalisa uku ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, 2024.

Lamarin dai ya haddasa hayaniya a majalisar yayin da waɗanda aka dakatar suka yi fatali da matakin nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262