Ganduje: Yadda Dakatarwa a Mazaba Ta Kori Shugabanni 3 a APC da PDP Ana Ji Ana Gani
Abuja - Yawancin ba a karewa da shugabannin jam’iyyu ta dadi a Najeriya, musamman idan ana maganar manyan jam’iyyun siyasa.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
A wannan rahoto na musamman, Legit Hausa ta waiwayi yadda dakatarwa a mazabu ta ci shugabannin jam’iyyun APC da PDP na kasa.
Dambarwar Ganduje a jam'iyyar APC
Mun kawo wannan ne ganin yadda wasu suka huruowa Abdullahi Ganduje wuta a jam'iyyar APC da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikin shekaru hudu rak, dakatarwa daga mazaba ta ci shugabanni akalla uku da suka rike ragamar APC mai mulki da PDP mai hamayya.
Shugabannin APC da PDP da aka dakatar
1. Adams Oshiomhole (APC)
Bayan rigimar Adams Oshiomhole da Godwin Obaseki, shugaban na APC bai dade sosai a kan kujerarsa ba, haka ya yi rashin sa’a a kotu.
Obaseki bai samu tikitin APC ba, amma a karshe shugabannin APC a mazabar Etsako sun dakatar da Oshiomhole, dolen shi ya sauka a 2020.
2. Prince Uche Secondus (PDP)
Prince Uche Secondus bai bar majalisar NWC ta dadi ba, dakatar da shugaban na PDP daga mazabarsa a jihar Ribas ta ga bayan shi.
Shugabannin PDP na mazabar Ikuru a Andoni sun kori Secondus, da aka je kotu a 2021 alkali ya tabbatar da ya tashi daga matsayinsa.
3. Dr. Iyorchia Ayu (PDP)
Jim kadan bayan zaben 2023 sai aka ji ‘yan jam’iyyar PDP a mazabar Igyorov a Gboko da ke Benuwai sun hadu sun dakatar da Iyorchia Ayu.
Tun da tsohon ministan ya rasa matsayinsa na zama ‘dan jam’iyya, ana ji aka gani Umar Damagum ya canji Ayu a majalisar NWC ta kasa.
Rikicin cikin gidan jam'iyyar PDP
Kwanaki rahoto na musamman ya zo cewa matashin ‘dan siyasa, Aliyu Kwarbai ya yi watsi da jam’iyyar PDP da ya dade yana goyon baya.
Duk da yadda ya yi suna wajen kare PDP a kafafen sadarwan zamani, sai aka ji ya fice daga jam’iyyar adawar saboda rigimar cikin gida.
Kwarbai bai ga amfanin zama a PDP idan har za a rika rufe kofa tare da irinsu Nyesom Wike ba wanda minista ne a gwamnatin APC.
Asali: Legit.ng